Tsohon Shugaban Matasan APC na neman takarar Gwamnan Gombe a NDC
Komawarsa NDC a cewarsa, na da nasaba da fatan samun adalci a zaɓen fid-da-gwani da kuma burinsa na ci gaba da hidimta wa al’umma cikin nagarta a sabuwar jam’iyyar.
Tsohon Shugaban Matasan Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sadiq Abubakar, ya koma jam’iyyar NDC inda ya fito neman takarar Gwamnan Jihar Gombe.
Ya shaida wa manema labarai a Bauchi ranar Alhamis cewa NDC na daga cikin jam’iyyun siyasa ’yan ƙalilan masu kima
A cewarsa, ya yanke shawarar komawa ADC me bayan tattaunawa a makusanta da abokan siyasa a makon da ya gabata inda ya yanke shawarar ficewa daga APC.
Komawarsa NDC a cewarsa, na da nasaba da fatan samun adalci a zaɓen fid-da-gwani da kuma burinsa na ci gaba da hidimta wa al’umma cikin nagarta a sabuwar jam’iyyar.
- Kotu ta yi wa fasto ɗaurin rai-da-rai kan fyaɗe ga ƙananan yara
- An fargabar cutar Sanƙarau ta kama mutum 105 a Katsina
Abubakar ya ce, “ADC ce jam’iyyar da kowane memba ke samun adalci, inda ba a yin ƙarfa-ƙarfa, domin fifita ra’ayin wasu.
“Duk hanyar da jam’iyyar ta zaɓa na fitar da ɗan takara, ta hanyar sasanci ko zaɓen fid-da-gwani, za mu karɓe shi hannu bibbiyu,” a cewarsa.