Tsohon shugaban NFF, Ibrahim Galadima, ya rasu yana da shekaru 78

Marigayin ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Tsohon shugaban NFF, Ibrahim Galadima, ya rasu yana da shekaru 78

Tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF,  kuma wanda ya kafa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Alhaji Ibrahim Galadima, ya rasu.

Ya rasu a ranar Asabar bayan fama da rashin lafiya, yana da shekaru 78 a duniya.

Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Kano Pillars ne, ya tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da ya fitar  ranar Asabar.

An haifi marigayin a ranar 15 ga watan Fabrairu, 1948, kuma ƙungiyar ta bayyana shi a matsayin fitaccen jami’in gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa kuma ɗaya daga cikin manyan mutane masu tasiri a harkar wasanni a Najeriya.

Sanarwar ta ce, “Ya kasance Shugaban NFF tsakanin shekarar 2002 zuwa 2006, inda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa harkar ƙwallon ƙafa ta Najeriya da kuma wakilcinta a matakin ƙasa da ƙasa.”

Ta kuma ce, “Ya kuma yi fice a matsayin Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin wasanni tun daga tushe har zuwa matakin ƙoli.”

Dangane da rawar da ya taka a Kano Pillars, sanarwar ta ƙara da cewa, “A matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Kano Pillars FC, Galadima ya aza tubalin da ya sa ƙungiyar ta zama ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin kwallon kafa a Najeriya.

“Jagorancinsa da ƙaunarsa ga wasan ƙwallon ƙafa za su ci gaba da kasancewa wani ɓangare na tarihin ƙungiyar.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa za a yu jana’izarsa a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10 na safe a Masallacin Waje da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano.

Ƙungiyar Kano Pillars FC, ta hannun Babban Manajanta, Ahmed Musa, da Shugabanta, Alhaji Ali Muhammad Umar, ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, gwamnatin Jihar Kano, al’ummar jihar da kuma ɗaukacin masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon kafa ta Najeriya.

Ƙungiyar ta kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya jiƙansa da rahama tare da bai wa iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.