Tsohon Shugaban Pakistan, Pervez Musharraf ya rasu

Musharraf da ke gudun neman mafakar siyasa a Dubai ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibitin, yana da shekara 79.

Tsohon Shugaban Pakistan, Pervez Musharraf ya rasu

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Kasar Pakistan na mulkin soji, Janar Pervez Musharraf, rasuwa.

Musharraf da ke gudun neman mafakar siyasa a Dubai, ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibitin, yana da shekara 79.

 

Hukumomin kasar sun ce Musharraf, wanda ya kasance na hannun Amurka wajen yaki da ta’addanci a yankin Asiya ya rasu ne bayan fama da jinya.

A shekarar 1999 Mista Pervez Musharraf ya kwace mulki cikin ruwan sanyi, inda kuma ya ci gaba aiki a matsayin Shugaban Kasa da kuma Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa ta Pakistan.Sau biyu Janar Pervez Musharraf ke jingine kundin tsarin mulki kuma ana zargin sa da murdiya a zaben raba gardama domin dawo da mulkinsa.Ana kuma zargin sa da yaushe hakki da kuma tsare ’yan adawa.

Amma duk da haka ya zama babban abokin Amurka a yankin Asiya a lokacin da Amurkar ta mamaye Afghanistan a shekarun 2011 domin yakar Taliban.

Matakin nasa ya haifar da rikici tsakaninsa da mayakan Islama, inda a lokuta da dama aka nemi hallaka shi.

Hakan kuma ya sa Pakistan ta samu tagomashin tallafi daga kasashen waje, lamarin da ya bunkasa tattalin arzikinta.

Wani masani ya ce, “Za a rika tunawa da Musharraf a matsayin shugaban kasa da ya jagoranci Pakistan a cikin mawuyacin hali.

“Shigar gwamantin Pakistan yaki da ta’addanci a zame mata…’” in ji shi a hirarsu da AFP.