Tsohon shugaban PDP da wasu sun koma APC a Yobe

Tsohon shugaban jam’iyyar adawa ta PDP Lawan Gana Karasuwa da wata tsohuwar ‘yar takarar Sanata Dakta Mairo Amshi  tare da wasu mabiyan jam`iyyar sun fice daga jam’iyyar sun koma APC a jihar Yobe. Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ne ya karbi sababbin ‘yan jam’iyyar a jiya Talata yayin kamfen da gwamnan ya jagoranta a birnin […]

Tsohon shugaban PDP da wasu sun koma APC a Yobe

Tsohon shugaban jam’iyyar adawa ta PDP Lawan Gana Karasuwa da wata tsohuwar ‘yar takarar Sanata Dakta Mairo Amshi  tare da wasu mabiyan jam`iyyar sun fice daga jam’iyyar sun koma APC a jihar Yobe.

Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ne ya karbi sababbin ‘yan jam’iyyar a jiya Talata yayin kamfen da gwamnan ya jagoranta a birnin Gashuwa da ke Yobe ta Arewa.

A jawabin tsohon shugaban PDP da ya koma APC ya ce, ya yanke shawarar koma wa jam’iyyar mai mulki ne ta APC ganin irin ci gaban da jam’iyyar ta samar a wannan gwamnati a duk fadin kasar.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta