Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda
Hatsaniya ta ɓarke a filin jirgin saman lokacin da ’yan sanda suka kama Mista Duterte.

’Yan sanda sun cafke tsohon shugaban ƙasar Philippines, Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talatar.
Mista Duterte ya faɗa komar ’yan sandan ne bisa sammacin Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kaɗan da saukarsa daga birnin Hong Kong.
- Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet
- Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya
Hatsaniya ta ɓarke a filin jirgin saman lokacin da ’yan sanda suka kama Mista Duterte, sakamakon tirjiya daga masu tsaron lafiyarsa da likitansa da kuma lauyoyinsa, wadanda ke zargin cewa an take masa haƙƙinsa da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi.
Fadar shugaban ƙasar Ferdinand Marcos ta ce tsohon shugaban na fuskantar tuhumar kisan ɗimbin jama’a a lokacin mulkinsa, wanda ya fake da yaƙi da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
A lokacin dai ya sha alwashin kawar da fataucin miyagun ƙwayoyi, amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’dama sun ce lamarin ya rikiɗe zuwa wani abu daban, inda ake zargin ’yan sanda da kashe dubban mutane, ciki har da waɗanda da ba su ji ba ba su gani ba.