Tsohon Shugaban Sojin Kasa, Ihejirika ya shiga APC

Janar Ihejirika shi ne Shgauban Rundunar Sojin Kasa a mulkin tsohon Shugaba Jonathan

Tsohon Shugaban Sojin Kasa, Ihejirika ya shiga APC

Jam’iyyar APC

Tsohon Babban Hafson Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Azubike Ihejirika ya shiga jam’iyyar APC mai mulki.

Mai magana yawun Buni, Mamman Mohammed ya ce Shugaban Kwamitin tsare-tsaren Jam’iyyar kuma Gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru da Shugaban Kwamitin Tuntuna na Jam’iyyar Hon. Farouk Adamu Aliyu ne suka gabatar da Ihejirika ga Buni ranar Juma’a.

“Shigowar Janar Ihejirika zai kara wa jam’iyyarmu karsashi a Jihar Abiya da ma daukacin yankin Kudu maso Gabas.

“Babban abin murna ne ganin Janar Ihejirika da wasu fitattun ’ya’yan yankin Kudu maso Gabas suna shigowa jam’iyyar domin kawo yankin kusa da Gwamnatin Tarayya.

“Muna sa ran ganin kara kafuwar APC a yankin,” inji Buni.