Tsohon Shugaban Zimbabwe na farko bayan ta sami ‘yancin kai Robert Mugabe ya mutu yana da shekara 95. Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ne ya sanar da mutuwar Mugabe a yau Juma’a. Rahotanni na bayyana cewa, iyalan Mugabe sun sanar da cewa, ya mutu ne bayan ya yi jinya. Shugaba Emmerson, ya ce tarihin kasa ba […]
Tsohon Shugaban Zimbabwe na farko bayan ta sami ‘yancin kai Robert Mugabe ya mutu yana da shekara 95. Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ne ya sanar da mutuwar Mugabe a yau Juma’a.
Rahotanni na bayyana cewa, iyalan Mugabe sun sanar da cewa, ya mutu ne bayan ya yi jinya.
Shugaba Emmerson, ya ce tarihin kasa ba zai taba mantawa da gwagwarmayar da Mugabe ya yi a lokacin rayuwarsa wajen gina Zimbabwe.