Tsohon soja I

Wani Bahadeje ne dan limami ya tafi aikin soja, da ya gama aikin ya dawo gida, mutane suka rika ce masa: “Sai ka yi liman.” Shi kuwa yana cewa amin. A kwana a tashi, rannan sai Allah Ya yi wa liman rasuwa, sai mutanen gari suka ce: “Ai ga tsohon soja dan liman, a kira […]

Tsohon soja I
Tsohon soja I

Wani Bahadeje ne dan limami ya tafi aikin soja, da ya gama aikin ya dawo gida, mutane suka rika ce masa: “Sai ka yi liman.” Shi kuwa yana cewa amin. A kwana a tashi, rannan sai Allah Ya yi wa liman rasuwa, sai mutanen gari suka ce: “Ai ga tsohon soja dan liman, a kira shi a yi masa tambaya a kan matsalar Sallah, idan ya amsa, sai a nada shi, ya gaji babansa.” Da ya zo, sai aka yi masa tambaya a kan kabli da ba’adi, aka ce masa idan mutum yana cikin Sallah, sai kabli da ba’adi suka kama shi yaya zai yi? Sai Bahadeje tsohon soja ya ce: “Ita kabli ana yin ta a tsaye, ita kuwa ba’adi ana yin ta zaune.”
Daga Tsalha Yaro Mabera