Tsohon tauraron Manchester United Sir Bobby Charlton ya mutu

Charlton daya ne daga fitattun ’yan wasan United da suka bayar da gudunmuwar da ba za a manta da shi ba.

Tsohon tauraron Manchester United Sir Bobby Charlton ya mutu

Tsohon tauraron dan kwallon duniya kuma daya daga cikin ’yan wasa mafi bajinta a tarihin Manchester United, Sir Bobby Charlton ya mutu.

Sir Bobby Charlton wanda ya mutu yana da shekara 86, ya taka rawar gani a gasar Kofin Duniya a 1966 da Ingila ta karbi bakunci.

Charlton ya buga wa tawagar Ingila wasa 106 da cin kwallo 49 kamar yadda alkalumma na tarihi suka nuna.

Ya dade a matsayin mafi bajinta a kasar kafin daga baya Rooney ya karba, sai kuma Harry Kane da ke rike da gurbin.

A shekara 17 da ya yi wa United tamaula, ya lashe kofin lik uku da European Cup da kuma FA Cup.

Iyalan Charlton sun sanar cewa ya mutu ne yana tsaka da bacci a kan gadonsa da sanyin safiyar Asabar.

A cikin watan Nuwambar 2020 aka bayar da sanarwar cewar Charlton ya kamu da cutar ciwon mantuwa.

United ta mika ta’aziyya ga iyalan Charlton da cewa “daya ne daga fitattun ’yan wasan kungiyar da suka bayar da gudunmuwar da ba za a manta da shi ba.”