Tsohuwa da Sabuwar Gwamnatin Jihar Katsina a kan sikeli
Yau wata takwas ke nan da aka samu canjin gwamnati a Najeriya, inda a Gwamnatin Tarayya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya amshi ragamar mulki daga hannun tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan. Haka ma ta kasance a Jihar Katsina, inda Alhaji Aminu Bello Masari na Jam’iyyar APC ya amshi tasa ragamar mulkin daga […]
Yau wata takwas ke nan da aka samu canjin gwamnati a Najeriya, inda a Gwamnatin Tarayya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya amshi ragamar mulki daga hannun tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan. Haka ma ta kasance a Jihar Katsina, inda Alhaji Aminu Bello Masari na Jam’iyyar APC ya amshi tasa ragamar mulkin daga hannun Barista Ibrahim Shehu Shema na Jam’iyyar PDP, bayan ya kwashe shekaru takwas a gadon mulki.
A matakin Gwamnatin Tarayya, Shugaba Buhari, kamar yadda ta tabbata a zahirance, ya amshi gwamnati ce tabarbararra, domin kuwa shaida ta tabbatar da yadda tsohuwar gwamnati ta barnata dukiyar kasa, wanda haka ya kara ta’azzarar da lalacewar tattalin arzikin kasa, harkar tsaro ta kara dagulewa da tabarbarewa. Haka ma sauran sassan rayuwa da kowane al’amari ya zama koma-baya. Dalili ke nan Buhari ya jajirce, ya baza komarsa, inda a yanzu haka an fara farautar wadanda suka yi halin kusu, suka sace dukiyar da ta kamata a yi wa talakawa aiki da ita, inda ya zuwa yanzu, an samu tabbacin cewa har ma an fara maido da irin wannan haramtattar dukiya zuwa asusun gwamnatin ta tarayya.
Abin kamar arashi, a Jihar Katsina ma, labarin bai canza da na Gwamnatin Tarayya ba, domin kuwa daga hawansa kujerar Gwamna, Masari sai ya yi koyi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya dora harsashi kuma ya dauki niyyar bunkasa al’ummar jihar, ta hanyar gudanar da ayyukan raya kasa. Sai dai inda gizo ke sakar shi ne, duk da cewa akwai wasu hanyoyi na daban da za a iya samun kudin shiga a jihar, gwamnatocin baya sun dogara ne kacokan ga daunin da jihohi da kananan hukumomi ke samu daga Gwamnatin Tarayya.
Dalili ke nan ma ya sanya jihar ta zama cikin rukunin jihohin da ake cewa su ne mafi talauci a kasar nan, inda dinbin matasa marasa aikin yi suka yi yawa. Haka kuma, sakacin na gwamnatocin baya ya sanya jihar da aka san ta da bunkasar tattalin arzikin noma da kiwo, amma aka bari wannan ya tabarbare, manoma ba su samun tallafin da ya kamata daga gwamnati. Maganar kasuwanci kuwa ya zama labari. Sauran harkoki kamar ilimi, ruwan sha da hanyoyi suka zama a lalace.
Masu kula da al’amuran yau da kullum sun tabbatar da cewa, idan ka debe gwamnatin marigayi Umaru Musa, wacce ta kwashe shekara takwas a gadon mulki, wacce ta gina hanyoyin raya karkara da birane, ta gina sabbi da gyara makarantu, gwamnatin da ta gaje shi sai ta ki ci gaba da wannan nau’i na raya kasa. An bayar da misali da yadda gwamnatin ta Shema cewa a tsawon mulkinta na shekaru takwas, ta amshi tsagwaron kudi kusan Naira tiriyan daya, amma ta kasa yin amfani da su yadda ya kamata ba wajen ayyukan gina al’umma.
Kamar yadda wani kwamitin bincike ya bayyana, ya ce cikin wannan adadin kudi kimanin Naira tiriliyan daya da tsohuwar gwamnatin ta samu, ta salwantar da kimanin Naira bilyan 47 ba bisa ka’ida ba, inda ma aka yi zargin cewa sace su aka yi. Hatta da gwamnatin ke cewa ta gina wasu hanyoyi, ta gina da yi wa makarantu kwaskwarima, an samu bayanin da ke cewa duk wani aiki da aka gudanar, ana yin aringizo wajen kudin kwangilarsa, kamar yadda aka rika zargin cewa kamfanonin da ke aiwatar da kwangilolin ma tuwona-maina ne kuma bas u yin ayyuka masu inganci.
An bayar da misali da cewa, a asusun hadin gwiwa da gwamnatin jiha ta tafiyar tsakaninta da kananan hukumomi, an barnata Naira biliyan 32, sannan ta hanyar hukumar raya karkara ta KASROMA, an salwantar da Naira biliyan 4.1, kamar kuma yadda aka yi amfani da Hukumar Raya Ilimin Mata, aka salwantar da kudade masu yawa.
Irin wannan barna da Gwamnatin Masari ta bankado, shi ya sanya ta tashi tsaye, ta sanya himmar kwato dukiyar talakawa da aka yi masu ha’incin kwashewa. Kamar dai yadda Gwamnatin Tarayya, a karkashin Muhammadu Buhari, take ta daukar himmar kwato dukiyar da jami’an tsohuwar gwamnati suka wawure.
Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sabuwar gwamnatin Jihar Katsina, karkashin jagorancin Aminu Masari za ta bambanta da wacce ta gabace ta, ta fuskar aiwatar da ayyukan raya kasa ga al’umma? Ba ma batun raya kasa ba, shin ko za ta samu kudin da za ta cin ma burin nata? Idan ma har za ta samu din, ko za ta aiwatar da ayyukan nata cikin adalci, ba tare da jami’anta sun nuna halin bera da gafiya ba?
Idan aka lura da yadda gwamnan yake kara nanata aniyarsa da kudurisa na gudanar da aiki wurjanjan, da kuma yadda yake nanata bin doka da oda wajen tafiyar da mulkinsa, da kuma yadda yake nuna cewa ba zai daure wa duk wani jami’i mai halin bera gindi ba, ana sa ran cewa kila kwalliya ta biya kudin sabulu.
Masu yakinin samun nasarar Gwamnatin Masari, sun kara kafa hujja da yadda ya fara aiwatar da wasu muhimman ayyuka, a cikin watanni takwas na farko da ya kama mulki. Misali, lokacin da ya hau mulki, gwamnan ya iske dinbin ma’aikata da suka yi ritaya amma an dauki lokaci ba a biya su hakkokinsu na giratuti da fansho ba. Wannan ta sanya tilas ya ciwo bashin Naira biliyan 11 daga Babban Bankin Najeriya, domin biyansu hakkokinsu. Ganin kuma yadda mafi yawan asibitocin kananan hukumomi suka lalace, ya zuwa yanzu ya dauki gyaransu, inda ya zabi manyan asibitoci guda uku da ke shiyyoyin Katsina da Daura da Funtuwa. Haka abin yake ga harkar samar da ruwan sha mai tsafta ga al’umma. An bayar da misali da garin Malumfashi, inda sama da shekara goma da ta wuce babu ruwan famfo. Ya zuwa yanzu an fara aikin gyaran ruwa a Katsina da Malumfashi da Dutsin-ma. Haka ma batun makarantu yake, gwamnatin ta shiga gyara da gina wasu, ganin yadda harkar ilimi ta shiga garari a jihar.
Idan dai matakin da Gwamna Masari ya dauka ya ci gaba, ana ganin cewa gwamnatinsa za ta bambanta da tsohuwar gwamnatin da ya gada, duk da cewa akwai manyan kalubale a gabansa. Bisa ga haka, ya zama dole a ba gwamnan shawarwari kamar haka:
Lallai ya kamata Gwamna Masari ya gane cewa jiharsa, ita ce jihar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, don haka sauran gwamnoni da ma al’ummar Najeriya za su maida hankalinsu a kanta. Idan ya gyara ta, zai samu yabo kuma ya zama abin alfaharin talakawa da ma shi kansa Shugaban kasa. Na biyu, ya kamata ya sanya ido sosai, kada ya sake ya ba bara-gurbin jami’ai dama su rika yin halin bera a gwamnatinsa. Na uku, ya nisanci yin tarayya da wasu batattun ’yan kasuwa da ’yan kwangila, wadanda babu abin da suka sa gaba sai illata dukiyar talakawa.
Muna rokon Allah Ya ba shugabanninmu basira da karfin gwiwar aiwatar da kyakkyawan mulki ga al’umma. Amin!