Tsohuwa da saurayin jikarta
Wani saurayi ne ya ga wata budurwa ya ji yana sonta da aure, sai ya tambaya aka shaida masa cewa tana hannun kakarta ce. Sai ya je gidan don su gaisa, ya shaida mata cewa: “Inna, Maryam ce na gani nake so da aure.” Sai tsohuwa ta ce: “A’a yaro an ba da ta.” Da […]
Wani saurayi ne ya ga wata budurwa ya ji yana sonta da aure, sai ya tambaya aka shaida masa cewa tana hannun kakarta ce. Sai ya je gidan don su gaisa, ya shaida mata cewa: “Inna, Maryam ce na gani nake so da aure.” Sai tsohuwa ta ce: “A’a yaro an ba da ta.” Da zai tafi sai ya ciro damen kudi sababbi ya mika mata ya ce ta sayi goro. Da ta ga kudi cus, sai ta ce: “tsaya yaro, ka dan gidan wane ne?” Ya ce shi dan gidan Malam Haruna ne. Ta ce na wajen Malam Saleh, ya ce, eh. Ta ce: “Allah Sarki! Malam Saleh mutumin kirki ne, lokacin da muke yara idan muka ja fada shi ke tare mana!”
Daga Anisa Adamu Abdullahi Daura, 07067716102