Tsohuwa mai shekara 100 ta warke daga coronavirus
Tsohuwar ta shafe mako biyu a killace kafin daga bisani a sallame ta kuma ta koma gidanta da ke Yangon.
An samu wata tsohuwar mata a Myanmar mai shekara 100 a duniya, Daw Thein Khin ta warke daga cutar Coronavirus.
Daw Thein Khin, ita ce bil Adama mafi tsufa da ta warke daga cutar a Myanmar kamar yadda wani dan siyasa a yankin, Wai Phyo Han ya wallafa a shafinsa na Facebook.
- Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar coronavirus
- ‘Yan wasan Firimiyar Ingila 5 sun kamu da Coronavirus
Tsohuwar matar ta shafe mako biyu tana jinya kafin daga bisani a sallame ta daga cibiyar killace masu cutar ta Yoma Yeiktha kuma ta koma gidanta da ke Yangon a ranar Alhamis.
Wani rahoto da jaridar BBC ta wallafa ya ce, yankin Yangon na cikin dokar kulle yayin da alkaluman masu kamuwa da cutar ke karuwa, inda a yanzu mutum 29,314 masu dauke da ita, sannan 665 sun mutu.