Tsohuwa ’yar shekara 112 ta shafe shekara 95 tana shan taba
Wata tsohuwa ’yar kasar Nepal ta keta binciken da kimiyya ta gano, cewa taba na kassara rayuwa, sabanin haka ta shafe shekara 95 tana banker hayakin taba; kuma a halin yanzu tana da shekara 112 .Matar mai suna Batuli Lamichhane, ta ce ta shafe wadannan shekaru 95 tana zukar taba, inda ta damfaru da tsananin […]
Wata tsohuwa ’yar kasar Nepal ta keta binciken da kimiyya ta gano, cewa taba na kassara rayuwa, sabanin haka ta shafe shekara 95 tana banker hayakin taba; kuma a halin yanzu tana da shekara 112 .
Matar mai suna Batuli Lamichhane, ta ce ta shafe wadannan shekaru 95 tana zukar taba, inda ta damfaru da tsananin son shan sinadarin nicotine. Wannan mata na rike tabarta ne da daukacin dunkulen hannunta, sabanin yadda mashayan taba ke rikewa da yatsun su.
“Ban dmau da nisan shekaruna ba,” inji ta. Sai dai na san na tsufa. Na jkuma ga sauyi iri-iri a rayuwata,” a cewarta.
A cikin watan Maris mai zuwa ake sa ran za ta cika shekara 113. Macen da ta fi kowa tsufa da nisan shekaru a wannan duniya, an ce shekarun ta 116, kuma tana zaune a garin Brooklyn, sunanta Susannah Mushatt Jones.
Babban dan wannan tsohuwa shekararsa 85, kuma yana da tattaba kunne. Sauran ’ya’yanta hudu duk sun mutu a gaban idonta.
Duk da cewa, wannan tsohuwa na samun tangarda da in-ina a maganarta, amma tana iya yin ayyukan gidanta da kanta.
Sakamakon girgizar kasa da aka yi a kasar Nepal, tsohuwar ta ki barin gidanta day a rufta. Tana samun tallafi daga dakin addin Hindu.
Wannan tsohuwa ta bada tabacin cewa, sirrin rayuwarta na tattare da ayyukan gida da take gudanarwa da kanta, tare da shan taba sigari kara 30 a kullum, sabaninb yadda kimiyya ta tabbatar cewa, zukar taba na lahanta rayuwar mutane. “Mutanen wannan zamanin suna cike da dugunzuma cikin damuwa da gajiya. Sannan wadanda ba sa yin wani aiki ko suke zaman banza, ba za su yi tsufa da nisan shekaru ba. Don haka akwai bukatar mutum ya rika kazar-kazar da kawar da duk wata damuwa da za ta haifar da gajiyawa,” a cewarta.