Tsohuwar da ta fi kowa shekaru a Japan ta mutu
Wata tsohuwa Nabi Tajima, wanda aka gano ta fi kowacce mace tsufa ta mutu ne tana da kimanin shekaru 117 a kasar Japan kamar yadda majiyar ABC News reports ta sanar. Wani jami’i dan birnin kasar Japan dake garin Kikai ya ce, Nabi Tajima ta mutu ne a daren ranar Asabar a inda ta ke […]
Wata tsohuwa Nabi Tajima, wanda aka gano ta fi kowacce mace tsufa ta mutu ne tana da kimanin shekaru 117 a kasar Japan kamar yadda majiyar ABC News reports ta sanar.
Wani jami’i dan birnin kasar Japan dake garin Kikai ya ce, Nabi Tajima ta mutu ne a daren ranar Asabar a inda ta ke jinya a asibitin tun a watan Janairu.
An haifi Misis Tajima a ranar 4 ga watan Agusta 1900, rahoton ya bayyana Tajima ta mutu ne ta sama da jikoki 160 da magada a duniya.
Tajima haifaffiyar birnin Kikai dake unguwar Kagoshima a garin Kyushu, wanda ya ke kudancin kasar Japan a cikin daya daga cikin hudu na tsibirin kasar.
Misis Tajima, ta zama tsohuwar da ta fi kowa shekaru a watanni bakwai da suka gabata bayan mutuwar biolet Brown ’yar kasar Jamaica.