Tsohuwar da ta shafe shekara 32 tana maganar sa’a guda kacal duk rana

Ta kasance tana yin shiru na tsawon sa’o’i 23 a rana, tana yin hutun awa daya ne kawai da tsakar rana.

Tsohuwar da ta shafe shekara 32 tana maganar sa’a guda kacal duk rana

Saraswati Devi

Wata tsohuwa ‘yar shekara 85, mai suna Saraswati Devi za ta kawo karshen alkawarin da ta yi na yin shiru na tsawon shekara 32 da ta yi da kanta, wanda ya ba ta damar yin magana na tsawon sa’a guda kawai a rana.

Saraswati Devi, wacce aka fi sani da ‘Mauni Mata’, ta fara alkawarin shiru da harshen Inidiyanci ‘maun brat’ a 1992.

Ta sadaukar da rayuwarta ga abin bautarta ‘Lord Ram’ bayan mutuwar mijinta a 1986 kuma ta shafe mafi yawan lokutanta a aikin hajji.

A 1992, ta isa birnin Ayodhya a cikin Jihar Uttar Pradesh a Indiya, inda ta ziyarci Mahant Nritya Gopal Das, shugaban ginin Ram Janmabhoomi Trust, wanda yake wajen tarihi a kasar Indiya, wanda ya umarce ta da ta kewaya Dutsen Kamtanath a matsayin alamar sadaukarwa ga Ubangiji Ram.

A ranar 6 ga Disamba, a daidai wannan rana da aka rusa Masallacin Babri a Ayodhya, Saraswati ta gana da Swami Nritya Gopal Das, babban shugaba a wani yanki na Mani Ram Das Ki Chabani a cikin garin Ayodhya, kuma hakan ya sa ta nuna masa kwarin gwiwa, har ta sha alwashin daina magana har sai an gina sabon wajen bauta da aka kebe ga Ram a cikin birnin.

Alkawarinta zai kare a karshen wannan watan, tare da kaddamar da wajen bauta na Ram Mandir a Ayodhya.

“Bayan rushewar masallacin Babri Masjid, surukata ta ziyarci Ayodhya kuma ta dauki alkawarin kin yin Magana har sai an gina Ram Mandir,” in ji daya daga cikin surukai na Mauni Mata.

“Ta kasance tana yin shiru na tsawon sa’o’i 23 a rana, tana yin hutun awa daya ne kawai da tsakar rana.

“Sauran lokutan takan yi magana da mu ta hanyar rubutu da alkalami da takarda.

“Yawancinmu muna fahimtar yaren kuramenta. Amma takan rubuta rikitattun jimloli a takarda.”

Duk da shafe sa’o’in ba tare da magana ba a kowace rana amma har yanzu tana taimaka wa danginta sosai, sai dai a 2020, lokacin da Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi ya ba da sanarwar gina Ram Mandir a hukumance, daga nan tsohuwar ta daina magana gaba daya.

Saraswati Devi ta ziyarci fitattun wuraren bauta na Hindu a Indiya a cikin shekaru 32 da suka gabata yayin da ta ci gaba da yin shiru, kuma ta sadaukar da kai ga Ubangijinta Ram ta kai kusan matsayi na almara.

A ranar 22 ga Janairu, lokacin da za a kaddamar da Ram Mandir, za ta kawo karshen yin shiru ta hanyar furta kalmarta ta farko cikin sama da shekaru 30, tana shewar murna da kalmar indiyanci ‘Ram Naam’.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume