Tsohuwar Gwamnatin Kebbi ta bar bashin Naira biliyan 83 – Dodo

Tsohuwar Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin jagorancin toshon Gwamna Sa’idu Usman dakingari ta bar bashin Naira biliyan 83 ga gwamnati mai zuwa. Bayanin haka ya fito ne daga bakin jami’in hulda da ’yan jarida na riko na sabon Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sani Dodo a lokacin da yake yi wa ’yan jarida bayani game da […]

Tsohuwar Gwamnatin Kebbi ta bar bashin Naira biliyan 83 – Dodo
Tsohuwar Gwamnatin Kebbi ta bar bashin Naira biliyan 83 – Dodo

Tsohuwar Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin jagorancin toshon Gwamna Sa’idu Usman dakingari ta bar bashin Naira biliyan 83 ga gwamnati mai zuwa.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin jami’in hulda da ’yan jarida na riko na sabon Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sani Dodo a lokacin da yake yi wa ’yan jarida bayani game da yanayin da jihar take ciki.
Alhaji Sani Dodo ya ce wannan bashin ya kunshi Naira biliyan 21 na tsagwaron bashi sai kuma Naira biliyan 47 na bashin ayyukan da ake gudanarwa sai kuma Naira biliyan 15 na ayyukan da aka amince a aiwatar amma ba a soma ba.
Alhaji Sani Dodo ya ci gaba da cewa a kan haka ne sabon Gwamnan Jihar Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya nada wani kwamiti da zai dubi yawan bashin da tsohuwar gwamnatin ta bari tare da tantace kaddarorin da gwamnati ke da shi.
Alhaji Sani Dodo ya ce an zabi Alhaji Mohammed Kwaido tsohon Akanta Janar na Jihar ya jagoranci kwamitin, wanda zai kunshi jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati da sauransu.
A wani labarin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya amince da nadin Alhaji Sulaiman Mohammed Argungu tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi a matsayin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamna, wannan shi ne mukami na farko da Gwamnan ya amince da shi tun rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar.