Tsohuwar Kwamishina a Kano Zubaida Damakka ta rasu
Har zuwa lokacin rasuwarta, ita ce Manajar Kamfanin Madara na L&Z.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Allah Ya yi wa Barista Zubaida Damakka Abubakar rasuwa a wannan Asabar din.
Ta rasu ne yau Asabar bayan ta yi wata ’yar takaitacciyar jinya a Abuja.
- An harbe mutum 2 wajen warwason kayan abinci a Taraba
- Gwamnatin Tarayya ta ninka kudin makarantar daliban sakandire
Za a yi jana’izar ta a gobe Lahadi da karfe 9 na safe a gidansu da ke Unguwar Gwammaja a birnin Kano.
Marigayiyar tsohuwar kwamishina ce a Ma’aikatar Harkokin Mata da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-Tsare ta Jihar Kano.
Haka kuma, har zuwa lokacin rasuwarta, ita ce Manajar Kamfanin Madara na L&Z.
Aminiya ta ruwaito cewa, Barista Zubaida na daya daga cikin kwamishinoni biyar da tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sauke a watan Oktoban 2017.