Tsohuwar matar wani alkali ta kashe shi a Kebbi
Kotu ta yanke hukuncin rataya ga tsohuwar matar wani alkali kan laifin hallaka shi.
Babbar Kotun Jihar Kebbi ta yanke hukuncin rataya ga tsohuwar matar wani alkali kan laifin hallaka shi.
Mai Shari’a Umar Abubakar ya yanke wa Farida Abubakar hukuncin ne kan laifin soka wa tsohon mijinta, marigayi Mai Shari’a Muhammed Attahiru Ibrahim Zagga, wuka a mararsa da wuyansa da kuma hannunsa, har ya rasu.
A yayin shari’ar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu 12 da hujjoji takwas, ciki har da hijabin wadda aka gurfanar, dauke da jini, wadanda ake kara kuma sun gabatar da hujjoji guda biyu a gaban kotun.
Alkali ya bayyana cewa masu kara sun gamsar da kotu cewa Farida na da hannu a kisan tsohon mijinta, don haka ya yanke mata hukuncin hanyar rataya kan laifin aikata kisa.
- Matar aure ta kashe mijinta da tabarya
- Katse lantarkin Najeriya: NLC da kamfanin TCN sun sa zare
- Yajin Aiki: Shugaban ’Yan Sanda ya gargaɗi NLC da TUC
Hakazalika ya yanke mata hukuncin daurin shekara bakwai kan laifin yi wa mamacin rauni da makami.
A ranar 4 ga Yuni 2024 aka yanke hukuncin bayan an fara gurfanar da ita a ranar 26 ga Yuli, 2023 kan aukuwar abin a ranar 25 ga Agusta 2022.
Lauya mai kare Farida ya roki a yi mata sassauci saboda wannan ne karon farko da ta aikata laifi kuma tana da karamar ’ya da ke bukatar kulawar mahaifiya, sannan ita ke kula da iyayenta da suka manyanta.
Sai dai lauyan masu kara ya bukaci a yi mata hukunci mai tsauri yadda alkali ya ga ya dace, domin hakan y zama darasi ga wasu.
Alkali ya shaida wa bangarorin cewa babu zabi a kan hukuncin laifin, musamman kasancewar ta kashe tsohon mijinta ne a lokacin da yake ma’aikacin shari’a.
A karshe dai lauyan wadda ake kara ya ce za su daukaka hukuncin zuwa kotun daukaka kara da ke Sakkwato.