Tsohuwar ’yar majalisa ta tallafa wa makarantu 15

Tsohuwar ’yar Majalisar Wakilai mai wakiltar Kaltungo da Shongom  da ke Jihar Gombe, Hajiya Binta Bello ta tallafa wa makarantu 15, inda ta tallafa wajen gyara ajujuwa 45 da suka lalace da kuma samar da kayan koyo da koyar da karatu. Makarantun sun hada da ta Farin Kasa da Sakandaren Gwamnati ta Burak wadanda aka […]

Tsohuwar ’yar majalisa ta tallafa wa makarantu 15

Wasu daga cikin ajujuwan da ta gina

Tsohuwar ’yar Majalisar Wakilai mai wakiltar Kaltungo da Shongom  da ke Jihar Gombe, Hajiya Binta Bello ta tallafa wa makarantu 15, inda ta tallafa wajen gyara ajujuwa 45 da suka lalace da kuma samar da kayan koyo da koyar da karatu.

Makarantun sun hada da ta Farin Kasa da Sakandaren Gwamnati ta Burak wadanda aka samar musu da kujerun zama da kayayyakin aiki.

Da yake zagawa da manema labarai, hadiminta Mista Simon Dauda ya ce ayyukan an faro su ne a watan Agustan bana duk da ba ta majalisar.

Ya ce a makarantar Farin Kasa, wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa cewa ta ga yara suna daukar darasi a kan duwatsu da karkashin bishiya ne ya sa ’yar majalisar ta tallafa don inganta ilimi.

Ya kara da cewa wannan ne karo na shida a yankin inda take samar da kujeru da kayayyakin aiki a makarantun baya ga ayyukan irin na ’yan majalisa na mazabu da ta yi a bangarorin ilimi da kiwon lafiya saboda kaunarta ga al’ummar mazabarta.

Da yake zantawa da manema labarai, Dagacin  Burak, Mista Gondak Garba, ya ce ba su da abin da za su ce da Binta Bello sai godiya kan yadda take kai dauki musamman a Sakandaren Gwamnati.

Shi ma a nasa jawabi wani shugaban al’umma a yankin Adamu Umaru gode wa Binta Bello ya yi a madadin al’ummar yankin, inda ya ce shugaba ce a bar koyi wacce ta jima tana ayyukan raya kasa musamman a bangaren ilimi.