Tsohuwar ’yar wasan Super Falcons ta koma namiji
Tsohuwar ’yar wasan kwallon kafa ta mata ta kasa watau Super Falcons mai suna Iyabo Abade wacce ta dade tana fama da lalurar mata-maza a yanzu ta samu nasarar komawa namiji bayan Likitoci a Amurka sun yi mata aiki. Asali ma yanzu ta canza suna daga Iyabo Abade zuwa James Johnson. A shekarar 2004 ne […]

Tsohuwar ’yar wasan kwallon kafa ta mata ta kasa watau Super Falcons mai suna Iyabo Abade wacce ta dade tana fama da lalurar mata-maza a yanzu ta samu nasarar komawa namiji bayan Likitoci a Amurka sun yi mata aiki. Asali ma yanzu ta canza suna daga Iyabo Abade zuwa James Johnson. A shekarar 2004 ne aka fara yi mata aiki amma sai a bana ake sa ran kammalawa. Iyabo (ko kuma James) ta samu zantawa da wasu ‘yan jaridu akan batutuwa da dama. Ahmed Garba Mohammed ne ya lalubo tattaunawar a yanar gizo inda ya fassara don amfanin masu karatun Aminiya kamar haka:
Tambaya: Yanzu da ka koma namiji daga mace, yaya kake gudanar da wasan kwallo a tsakanin mazaje?
Iyabo: A gaskiya na godewa Allah da ya nuna mini wannan lokaci. Na yi duk iya kokarin ganin na samu nasara a harkar kwallon kafa tun bayan da na koma namiji amma abin takaici ban samu wadanda suka tallafa mini ba. Kai hatta Hukumar Kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ba ta nuna min kauna ba. An bar ni ne kawa ina ta gararamba babu wani tallafi da na samu daga wajenta sai dai n ace nag ode Allah. da muke magana babu wani abu da ya kankama sai dai na ce na gode Allah.
Na sha zuwa kulob-kulob da dama a sassan duniya a matsayin gwaji. Bayan sun gwada ni kuma sun tabbatar na iya kwallo, da zarar sun dauke ni kafin wani lokaci sai a fara nuna mini wadansu halaye marasa kyau musamman yadda suke daukata a matsayin mace a da. Wasu ma sukan rika zolayata a matsayin mace duk da sun san yanzu na koma namiji kamar su.Na yi duk kokarin da zan yi don boye wa kulob da dama halin da nake ciki musamman ba na so na fada musu cewa ni ne Iyabo Abade a da amma da zarar sun gudanar da bincike suka gano cewa ni ne Iyabon da na taba yin kwallo a kulob din Crown FC ko na Plateau United daga lokacin sai ka ga sun fara nuna mini bambanci da kuma kyama. Duk da na koma kulob din ne a matsayin James Johnson, ba Iyabo ba, amma sukan rika zolaya ta hanyar yi mini tambayar “shin zan iya buga kwallo a tsakankanin maza?”, yin haka kuma ba karamin bata min rai yake ba. Sun manta cewa sai da aka yi min gwaji aka tabbatar na kware kafin su dauke ni. Abin tambaya a nan shi ne me ya sa tun farko suka dauke ni in sun san ba zan iya yin kwallo tare da su ba? Su makafi ne? Me ya sa sai daga baya idan sun fahimci halin da nake ciki suke nuna mini bambanci? Ni dai na gode Allah da yadda ya halicce ni kuma haka Allah Ya so, kuma ba na nadama a kan halin da na tsinci kaina.
Tambaya: Yaya dangantakarka take a yanzu da takwarorinka mata ’yan wasan Super Falcons?
Iyabo: Da yawa daga cikinsu suna girmama ni, musamman ganin mun yi zama tare kuma mun buga kwallo tare. Suna mutunta ni kuma ba sa nuna mini bambanci musamman ganin mun yi zama tare da su a lokaci mai tsawo. Sai dai a lokacin da suka samu labarin na koma namiji daga mace da yawa sun kadu, don wasu ma ba su taba tsammanin akwai wata halitta mata-maza a doron kasa ba.
Amma daga baya sun yarda da ikon Allah, sun ce ba ni na halicci kaina ba. Haka suka dauki al’amarin kuma har yau muna huldar arziki a tsakanina da su.
Tambaya: Na tabbata likitoci sungudanar da yi maka aiki ne a bisa mataki zuwa mataki, a halin yanzu a wane mataki ake?
Iyabo: Wannan gaskiya ne. Tun cikin shekarar 2004 aka fara yi mini aiki a matakin farko. A shekarar 2009 kuma na koma inda aka yi mini aiki a mataki na biyu sannan a shekarar da ta wuce watau ta 2012 ake sa ran yi mini aiki a mataki na uku kuma na karshe inda zan kasance cikakken da namiji amma saboda halin rashin kudi ta sa har yanzu ban samu damar komawa don a yi mini aikin ba. Na bazama don neman tallafi daga kowane bangare don ganin na samu kudin da zan koma Amurka. Amma babbar matsalar da nake fuskanta ita ce ta rashin kudi. Yanzu na shiga halin ni ’yasu. Kimanin wata bakwai kenan nake safa da marwa zuwa Hukumar Shirya Wasanni ta kasa (NSC) don ta tallafa mini amma abin ya ci tura. Na rubuta wasikun neman tallafi sun fi a kirga kuma na aika su duk inda nake tunanin za a kawo mini dauki amma har yanzu da muke wannan hira da kai babu abin da ya shigo hannuna. Don haka yanzu na yanke shawarar karkata akalata zuwa wani bangaren walau na neman taimako a wajen masu hannu da shuni ko daidaikun mutane na su yi wa Allah su taimake ni don ganin na fita daga cikin wannan kangi.
Abin takaici tun lokacin da tsohon Shugaban Hukumar Kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) Sani Lulu yake shugabanci na rubuta wasika kuma ya nuna zai taimaka min. A wancan lokaci ya ce “kawo wasikarka zan yi kokari na ga mun taimaka maka” amma bayan ya sauka sai aka nemi wasikar kasa ko sama aka rasa wai ta bata. Kuma har yanzu batun ya shiririce. Da ba don taimakon da nake samu daga wajen ’yan uwa da abokan arziki ba, ba san yadda zan yi ba wurin tafiya Amurka Likitoci na cigaba da duba ni a lokaci zuwa lokaci.
Tambaya: Kamar nawa kake bukata don cigaba da yi maka aikin?
Iyabo: Ina bukatar akalla Naira miliyan 12. Wadannan kudi su ne za su sa a yi mini aiki a matakin karshe. Likitoci sun fada mini ina bukatar in kwashe akalla wata goma sha biyu a Amurka don jinya kafin na dawo gida. Baya ga aikin, ina bukatar kudin da zan kama masauki da na abinci da na zirga-zirga da sauransu.
Tambaya: To a halin yanzu da ba a kammala aikin komawarka cikakken da namiji ba, yaya kake gudanar da rayuwarka a matsayin da namiji?
Iyabo: A gaskiya ina jin dadin yadda nake a halin yanzu. Amma zan so a ce an kammala yi mini aikin karshe da zai tabbatar mini da kasancewata cikakken da namiji. Duk da yake ba a kamala aikin ba amma al’aurata ta fi karkata a matsayin na da namiji fiye da na mace a halin yanzu don haka na yanke hukunci ni namiji ne a yanzu ba mace ba, kamar yadda likitocin suka tabbatar mini cewa yanzu ni namiji ne. Amma zan fi samun natsuwa ne da zarar an kamala yi mini aiki na karshe don tabbatar da kasancewata da namiji.
Tambaya: Kana da burin ganin ka kasance dan kwallo na farko da ya taba bugawa kungiyar kwallon kafa ta kasa bagaren mata Super Falcons da kuma ta maza Super Eagles amma burinka bai cika ba, yaya ka ji?
Iyabo: A gaskiya ban ji dadi ba. Don na dauki buga kwallo a matsayin rayuwa. Amma abin takaici shi ne yadda ban samu goyon bayan Hukumar shirya wasanni ta kasa (NSC) da kuma Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasa NFF ba. Da ’yan wasa masu lalura suna samun taimako daga wadannan hukumomi da ban tsinci kaina a irin wannan hali ba. Ko so ake na mika kokon barata ga kasar Amurka a kan wannan batu. Ina ganin idan nay i haka tamkar na kunyata kasar nan a idon duniya kenan, watau ga arziki amma an kasa tallafa mini.
Tambaya: Wadanne mutane ne suka tallafa maka tun farko kawo yanzu?
Iyabo: Ina mika godiyata ga tsofaffin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Alhaji Abba Gana da kuma Malam Nasir El-Rufa’i, a gaskiya sun tallafa mini. Sannan zan yi godiya ga Hajiya Turai ’Yar’adua kodayake ban samu taimakon kudi daga wajenta ba amma na samu shiga fadar shugaban kasa da ke Abuja ta dalilinta a lokacin da maigidanta yake Shugaban kasa. Yunkurin da ta yi na tallafa mini ya ci tura ne saboda rashin lafiyar Shugaba Umaru Musa ’Yar’adua. Duk da haka ta tura ni wajen wadansu don su taimaka mini amma har yau ban su yi mini komai ba.
Amma Matar shugaban kasa ta yanzu watau Patience Jonathan ba ta taimake ni ba. Duk kokarin da na yin a samu tallafi daga wajenta abin ya ci tura duk da yake mun fito daga yankin Neja-Delta tare. Abin ya daure mini kai a ce wata mata daga yankin Arewa ta fi nuna kauna da damuwa a kan matsalata fiye da wacce muka fito daga yanki daya. Ba san dalilin da ya sa Dame Patience Jonathan ba ta son taimako na ba.
Sannan ina mika godiya ga Cocin Family Worship da na Redeemed Christian Church of God bisa gudunmawar da suka ba ni na tafiya Amurka daga lokaci zuwa lokaci don likitoci su yi nazarin halin da nake ciki kawo yanzu.
Tambaya: Za ka amince idan kasar Amurka ta gayyaceka don ka rika buga mata kwallo?
Iyabo: Da gudu zan amince da haka. Ina ganin babu mahalukin da ba zai so a ce Amurka ta gayyace shi don buga mata kwallo ba musamman mu da muka kasance bakaken fata da suka fito daga yankin Afirka.
Tambaya: Mene ne shawararka ga masu dauke da lalurar mata-maza musamman wadanda suke jin kunyar shaida wa duniya halin da suke ciki kuma ba su samu dama irin taka ba?
Iyabo: Yanzu haka ina dauke da sunayen wadansu da na sani, kuma tuni na aikawa Likitana da ke Amurka sunaye da adireshinsu. Su biyu ne kuma dukkansu suna bugawa kungiyar kwallon kafa ta mata. Na nuna musu muhimmancin bayyana halin da suke ciki saboda a tallafa musu. A lokuta da dama nakan ji kamar na rataye kaina saboda takaici, amma idan na tuna ba ni na halicci kaina ba sai na manta da komai.
Tambaya: Kana da yunkurin kafa gidauniyar tallafawa mata-maza idan ka samu dama a nan gaba?
Iyabo: kwarai kuwa. Don hakan zai ba ni damar tallafawa masu irin wannan lalura a ciki da wajen kasa. Sannan ina da burin yada cibiyar zuwa sassan duniya. Akwai mata-maza da yawa a cikin al’umma amma saboda kunya da kuma yadda za a rika kallonsu ta sa ba kasafai suke bayyana halin da suke ciki ba. Alal misali akwai wani mata-maza a Jihar Delta da wadansu suka kusa hallaka shi bayan sun dauke shi a matsayin maye. Ka ga wannan bai dace ba kuma daukar alhaki ne. Don haka masu irin wannan lalura suke tsoron bayyanar da kansu a mafi yawan lokaci.
Tambaya: Idan mata suka fahimci kamarsu kake a da amma yanzu ka koma namiji, sukan guje ka?
Iyabo: A’a, mata na sona. Hasalima rububi suke na neman su yi kawance da ni. Duk inda na je mata kan so ni musamman ganin yadda nake da kyawun kira kuma ko sun san halin da nake ciki ba sa guduna.
Tambaya: Yaya balaguron da kuka yi zuwa Amurka a shekarar 2012 tare da kungiyar kwallon kafa ta mata ta Masarata Soccer Academy?
Iyabo: Gaskiya na ji dadi, don sun tuna mini lokacin da nake bugawa kungiyar kwallon kafa ta mata. Na yi wa kungiyoyin kwallon kafa na mata kwallo da dama ciki har da ta Karo All Star da ke Abuja.
Tambaya: Wane kalubale mutum kan fuskanta idan ya canza halitta walau daga mace zuwa namiji ko akasin haka?
Iyabo: A gaskiya akwai kalubale don kafin maza su amince da kai a matsayin namiji zai dauki lokaci. Haka abin yake ga bangaren mata, kafin su amince ka koma mace sai an dauki lokaci. To ka ga kamar abin nan ne da ake kira “ba ka ga tsuntsu kuma ba ka ga tarko”.
Tambaya: A wasu lokuta kakan ji kamar har yanzu kai mace ce?
Iyabo: kwarai kuwa, amma hakan bai hana ni cigaba da jin dadin rayuwa ba. Na fada maka cewa mata kan yi rububina kamar shahararren dan tseren Jamaika Usain Bolt saboda kaunata. Wannan ya tabbatar maka da cewa yanzu ni cikakken da namiji ne.
Tambaya: Za ka iya bayyana lokacin da ka fi jin dadi idan ka tuna a rayuwarka?
Iyabo: A gaskiya lokacin bai zo ba. Amma da zarar na tsinci kaina a kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles zan fi kowa murna.
Tambaya: Wane kira kake da shi ga Kocin Super Eagles, Stephen Keshi?
Iyabo: Ina yi masa fatan alheri. Kuma ina yi masa jinjinar lashe kofin Afirka da ya yi. Yakamata mu cigaba da taimaka masa da addu’a don ganin ya cigaba da daukaka martabar kasar nan a idon duniya.
(An dauki wannan tattaunawar daga jaridar Punch ta karshen makon da ya wuce)