Tsokaci a kan shawarar da Obasanjo ya ba Buhari
Assalam Edita, da fatan kana lafiya tare da sauran ma’aikatan aminiya. A matsayina na cikekken dan Nijeriya sannan mai zura ido domin kallon cigaban da kasarmu take fuskanta da ma ci baya, a bisa wannan dalili ne ma ya sa nake so na yi tsokaci a kan maganganun da tsohon shugaban Najeriya Cif Olushegun Obasanjo […]
Assalam Edita, da fatan kana lafiya tare da sauran ma’aikatan aminiya. A matsayina na cikekken dan Nijeriya sannan mai zura ido domin kallon cigaban da kasarmu take fuskanta da ma ci baya, a bisa wannan dalili ne ma ya sa nake so na yi tsokaci a kan maganganun da tsohon shugaban Najeriya Cif Olushegun Obasanjo ya yi a kan yanayin tafiyar da mulkin Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza kai wa izuwa yadda ’yan Nijeriya suke bukata daga gareta, to lallai ni a nawa ra’ayin zan iya cewa a cikin maganganun da tsohon shugaban ya fada akwai na gaskiya ta wani dangaren kuma akwai na son rai.
A takaice dai ga baki dayan maganar ta zama tamkar hanjin jimina, watau akwai na ci akwai na zubarwa, bisa la’akari da yadda kasarmu ke ciki a halin yanzu kuma a matsayin Olusegun Obasanjo na daya daga cikin manyan iyayen kasa wanda suka ga jiya kuma suka ga yau, gaskiya zan iya cewa fadan wannan maganar ta yi daidai duk da cewa wasu ’yan Najeriya sun kalli maganar da wasu fuskoki daban daban, to amma muddin kasa tana bukatar cigaba to lallai sai da masu iya fadawa gwamnatin kasar gaskiya, ko za ta dauka ko kuma ba za ta dauka ba.
A karshe ina kira ga gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da ta samo wata hanya da talakan Najeriya zai samu saukin rayuwa domin ni kaina yanzu haka da nake wannan maganar na kammala karatu a matakin N.C.E amma babu abun yi kuma kafin wannan gwamnatin ta hau karagar mulki cike nake da fatan samun abubuwan yi a ta dalilin wannan gwamnatin, to amma babu labari, kuma akwai miliyoyin mutane iri na ko a cikin garin da nake akwai daruruwan mutane da suka kammala karatu amma babu aikin yi to amma duk da rashin aiki da muke fama da shi tabbas mun samu zaman lafiya a yankinmu. Da fatan Allah Ya zaba mana duk abin da ya fi alkairi ga ’yan Nijeriya amin summa amin.
Prince Ya’u Adamu Bulkachuwa Jihar Bauchi. 09034444404, 09066738686