Tsokaci dangane da zumunci da muhimmancinsa (1)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya yi mana kyakkyawan nuni kan zumunci da muhimmancinsa, musamman a Suratu Nisa’i, aya ta 1. Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa, kuma ManzonSa, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, wanda ya ja hankalinmu dangane da matsayin kyautata zumunta, wadda ta […]
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya yi mana kyakkyawan nuni kan zumunci da muhimmancinsa, musamman a Suratu Nisa’i, aya ta 1.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa, kuma ManzonSa, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, wanda ya ja hankalinmu dangane da matsayin kyautata zumunta, wadda ta fuskarta ake samun karuwar arziki da tsawaitar rayuwa, kamar yadda ya zo a Hadisin da Buhari da Muslim suka ruwaito. Tsira da amincin Allah su kara tabbata gare shi da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, a makon jiya, mun gabatar da Hadisai na Abu Sufyaan da Amru dan Anbasah, inda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana matsayi da muhimmancin zumunta karara; ya daukaka matsayin, musamman tunda ya jera shi da wasu daga cikin manyan shika-shikan Musulunci, lamarin da ya tabbatar da matsayinsa da muhimmancinsa a cikin wannan addini, wanda Allah Ya saukar don jinkai ga al’ummar duniya gaba daya.
Yau ga ci gaba, tare da fata Allah Ya sa abin da aka karanta, aka fahimta, ya yi amfani duniya da Lahira, amin.
Wasu hujjoji na Musulunci sun kai matuka wajen karsasa al’umma dangane da matsayin sada zumunci, kuma sun ja kunne a kan ukubar da ke tare da yanke shi. Abu Ayyub al-Ansariy, (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Wani mutum ya ce, ‘Ya Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), fada mini wani aikin alheri da zan aikata don ya shigar da ni Aljanna.” Sai Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce masa, “Ka bauta wa Allah Shi kadai, kada ka hada kowa da Shi a cikin bautar; ka tsayar da Sallah; ka ba da Zakkah; kuma ka rike (sadar da) zumunci.” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito Hadisin).
Kamar wancan Hadisi da muka gabatar na hirar Abu Sufyaan da Hirkala, Sarkin Rum, wannan ma ya maimaita kansa ga wannan bawan Allah da ya yi wa Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), tambayar abin da zai taimaka masa ya shiga Aljanna. Shi ma ya nuna rike zumunci yana da babban matsayi, tunda an jero shi da manyan al’amurran addini, tun daga jigo, wato bauta wa Allah, Shi kadai ba tare da shirka ba; da tsayar da Sallah; da ba da Zakkah, lamarin da zai shigar da shi Aljanna ya nesantar da shi daga wuta. Allah Ya ba mu dacewa da yin abin da yake alheri.
A cikin bayanan da suka gabata, mun fahimci cewa rike zumunci da sadar da shi, yana taimakawa wajen samun yalwar arziki da rayuwa da rahamar Mahalicci a nan duniya da kuma gobe Lahira. Haka yana sanya kauna a tsakanin juna da yabo daga al’umma, amma kash!, yanke zumunci kuwa yana janyo wa mai yin sa bala’i da bakin ciki da kuncin rayuwa da kiyayyar Allah da ta al’umma da nesantar da shi daga Aljanna da kusantar da shi zuwa wuta, Allah Ya tsare mu daga gare ta. Wannan kuwa ya ishe mu hujja daga zancen Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), da ya ce, “Duk mutumin da ya yanke zumunci, ba zai taba shiga Aljanna ba.” (Buhari da Muslim suka ruwaito Hadisin).
Wani abin takaici game da mai yanke zumunci shi ne, in yana wuri, wato a cikin wata majalisa, yana iya janyo wa majalisar asarar samun rahamar Allah, kamar yadda wani Hadisi da Imam Baihakiy ya ruwaito a cikin littafin Shu’abul Iman cewa, “Jinkan Allah ba zai sauka a kan mutanen da a cikinsu akwai wanda yake yanke zumunci ba.”
Haka dai lamarin yake dangane da zumunci, har ma aka bayar da wani labari na babban sahabi Abu Huraira, (Allah Ya yarda da shi), wanda ya nuna cewa shi ba ya son a lokacin da zai yi addu’a cikin jama’a, ya kasance akwai wanda yake yanke zumunci, saboda gudun kada a ki karbar addu’ar kuma a ki zubo musu rahamar Allah. A wani taro da aka yi a ranar Alhamis (daren Jumu’a), za a yi addu’a, ya ce, “Ina rokon duk wanda ya san ya yanke zumunci, ya tashi ya ba mu wuri.” Ba wanda ya tashi, har sai da ya fadi haka sau uku, sannan sai wani matsakaicin mutum ya tashi ya tafi wajen wata gwaggonsa, wadda ya yanke zuwa wajenta na tsawon shekara biyu. A yayin da ya shiga wajenta, sai ta ce, “Ya dan dan uwana! Me ya kawo ka nan?” Ya ce mata, “Na ji Abu Huraira, (Allah Ya yarda da shi), ya ce kaza-da-kaza.” Sai ta ce masa, “Koma ka tambaye shi me ya sa ya ce kaza-da-kaza din nan.” (Abu Huraira) ya ce, ‘Na ji Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ana kai ayyukan ’yan Adam gaban Allah a kowane yammacin Alhamis, kafin Jumu’a, amma ba a karbar ayyukan wanda ya yanke zumunci.”
Musulmin da yake sane da abin da yake yi, kuma yake kwadayin samun rahamar Mahaliccinsa, ya samu tsira gobe kiyama zai girgiza, ya dimauta, idan ya ji irin wannan huduba, ta cewa ba za a karba masa ayyukansa na ibada ba, matukar yana yanke zumunci, kuma addu’arsa ba za a karba masa ita ba. Lallai zai kasance cikin takaici da bakin ciki, idan ya samu kansa cikin irin wannan hali, lamarin da zai sa ya kasance duk ayyukan da yake yi na ibada, sai su zama a wofi; in ya nemi rangwamen Mahaliccinsa ba za a karba masa ba. Saboda haka ko a mafarki bai kamata a samu Musulmin kirki yana yanke zumunci ba.
Yanke zumunci, zunubi ne wanda bai kamata Musulmin da zuciyarsa ke cike da shiriyar Allah da biyayya ga Allah, da za su haifar da samun amincewarSa, ya aikata shi ba, domin yana samar da fushin Allah da azabarSa. Hasali ma yana daga cikin manyan zunubai da Allah Yake yin horo ga wanda ya aikata su, a nan duniya da kuma Lahira, kamar dai yadda wani Hadisi ya bayyana cewa, “Babu wani zunubi mai tsanani da Allah ke azabtar da mai yinsa, a nan duniya, – ban da abin da zai same shi a Lahira – kamar (zunubin) yanke zumunci da cutar da mutane.” (Imam Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah suka ruwaito shi da isnadi ingantacce).
Yanke zumunci da zaluntar mutane, danjuma ne da danjummai, shi ya sa ma Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya fade su wuri daya. Yanke zumunci wani nau’in zalunci ne, wanda yake da karfi, musamman da yake na yanke wata igiyar ’yan uwantaka ne ta soyayya da kauna da shaukin juna.
Muna rokon Allah, Ya ba mu karfin zuciya wajen tabbatar da dankon zumunci a tsakaninmu da ma’abuta zumuncinmu, amin!
Ahmad Muhammad
Imel: [email protected]