Tsokaci dangane da zumunci da muhimmancinsa (2)
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya halicce mu kuma Ya sanya mu cikin Musulmi. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga bawanSa, ManzonSa, Annabi Muhammad, wanda ya kawo mana cikon addinin Musulunci, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa har zuwa Ranar […]
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya halicce mu kuma Ya sanya mu cikin Musulmi. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga bawanSa, ManzonSa, Annabi Muhammad, wanda ya kawo mana cikon addinin Musulunci, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, yau ma ga ci gaban tsokacinmu dangane da lamarin zumunci da fata Allah Ya sa mu amfana da shi, duniyarmu da Lahirarmu.
In ana biye da mu, a makon jiya, mun gabatar da Hadisin Abu Ayyub al-Ansari na mutumin da ya tambayi Manzon Allah (SAW) kan abin da zai yi ya shigar da shi Aljanna, aka jera masa wsu ayyukan ibada, wadanda cikinsu har da sada zumunci. Sannan ga Hadisin da Imam Baihaki ya ruwaito a cikin littafin Shu’abul Iman, mai cewa, “Jinkan Allah ba zai sauka a kan mutanen da a cikinsu akwai wanda yake yanke zumunci ba.” Wanda a dalilinsa ne ma aka gabatar da labarin sahabi Abu Huraira a yayin da ya bukaci duk wanda ya san ya yanke zumunci a taronsu da ya bar wurin saboda za a yi addu’a.
A karshe aka nuna cewa yanke zumunci wani nau’in zalunci ne wanda yake da girma, musamman da yake al’amari ne na yanke wata igiyar ’yan uwantaka ta soyayya da kauna da shaukin juna. Ga ci gaba:
Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bayyana irin narkon da ke fadawa kan lamarin yanke zumunci, inda ya ce, “kullin zumunci, wata sarkakkiyar dangantaka ce, wadda ta tuzgo daga Allah, Mai rahama. Zumunta ta ce, ‘Ya Ubangiji! An zalunce ni, ya Ubangijina! An yanke ni…’ Sai Allah Ya amsa mata, “Ba za ki wadatu ba, idan na yanke duk wanda ya yanke ki, kuma in kula da duk wanda ya kula da ke?” (Imam Buhari ne ya ruwaito shi).
Hasali ma dai Allah, Mai girma da daukaka, Ya daukaka matsayin kulla zumunci, Ya ba shi matsayin rahmu, wanda yake da tushe daya daga cikin sunayenSa na Arrahman, a yayin da Ya ce, “Ni ne Arrahman (Mai rahama – tausayi), kuma Na halitta rahmu (zumunta), Na ciro sunanta daga sunaNa. Duk wanda ya kula da ita, Zan kula da shi, kuma duk wanda ya yanke ta, Zan wofinta da shi.” (Hadisin kudsi, wanda Buhari ya fitar da cikin littafinsa Al-Adab Al-Mufrad, Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi sun ruwaito shi).
Wannan yana nuna wa Musulmi mai hankali, irin muhimmancin da sada zumunta ke da shi, musamman ma da yake Allah Zai kula da shi, Ya kare shi, idan ya kula da sha’anin zumunci. Zai dandani zakin jinkan Mahaliccinsa. Wanda kuwa ya yanke igiyar zumunci, zai shiga cikin matsalar da bai san iyakarta ba, musamman domin Allah Zai wofinta da shi, ya daidaita. Allah Ta’ala Ya kare mu daga fadawa cikin ramin yanke zumunci.
Shi Musulmi na kwarai yana kula da zumunci ne, ya rike shi sosai a karkashin koyarwa ta addinin Musulunci, ta yadda ba zai bari kyale-kyalen duniya na dukiya ko iyali (mata da’ya’ya) ya dauke hankalinsa, har ya juya wa danginsa baya ya kyale su, ya ki girmama matsayinsu ko ya taimaka musu ba. Zai kula da su ne gwargwadon yadda tsarin addininsa na Musulunci ya koyar da shi, wato bayan mahaifansa, wadanda uwa ita ce kan gaba wajen kulawa a matakai biyu; sai uba, sannan dangi na kusa da na nesa.
Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi tambaya, “Ya Manzon Allah! Wa ya fi cancantar kulawata?” Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Mahaifiyarka; mahaifiyarka; mahaifiyarka; sannan mahaifinka; sannan danginka na kusa.” (Buhari da Muslim suka ruwaito Hadisin).
Duk Musulmin da yake kyautata wa danginsa, yana samun lada ribi biyu ne: daya don zumunci, dayan kuma don kyautatawar da ya yi, lamarin da zai karfafa masa gwiwar kula da dangin nasa a duk lokacin da suke da bukata kuma yana da halin da zai taimaka musu din. Wannan shi ne ake kira dadi biyu, wato ga dai Allah Yana farin ciki da shi, ga kuma danginsa suna na’am da al’amarinsa cikin soyayya da girmamawa.
Wannan dabi’a ita ce Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bukaci Musulmi da su yi kuma ya karsasa lamarinsu a kan haka, kamar dai yadda ya zo a wani Hadisin Zainab Assakafiyya, matar Abdullahi dan Mas’ud, (Allah Ya yarda da su). Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ya ku mata! Ku ba da sadaka koda daga cikin gwala-gwalanku ne.”
Jin haka ya sa Zainab ta tafi wajen mijinta ta bukaci ya je wajen Manzon Allah (SAW) ya tambaya ko ya dace ta ba shi sadaka tunda ba shi da wadata, sai ya ba ta iznin ita ta je ta tambaya. A lokacin da ta tafi wajen Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ta iske wata mata daga cikin Ansarawa, ita ma ta je da kwatankwacin bukatar ba mijinta sadaka. Sai suka aiki Bilal, (Allah Ya yarda da shi), don ya tambayo musu Manzon Allah (SAW) kan wannan bukata tasu, sai Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Za su samu lada biyu; ladar kyautata zaman tare da kuma ta sadaka.” (Buhari da Muslim suka ruwaito Hadisin).
Sau da yawa Manzon Allah (SAW) yakan karfafa bayar da muhimmanci kan abin da ya danganci kyautatawa ga dangi da zarar bukatar haka ta samu. A yayin da aka saukar da aya ta 92 cikin surar Al-Imran, mai cewa, “Ba za ku samu kyautatawa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so…”, sai sahabi Abu dalha (RA) ya tafi wajen Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ya Manzon Allah! Ga abin da Allah Ya ce (a wannan aya), ni kuma abin da ya fi soyuwa gare ni a cikin dukiyata ba kamar gonata Bayraha (gonarsa ce ta dabino da take da rijiya mai ruwan dadi, wadda har Annabi kan shiga ya sha ruwan), na bayar da ita sadaka saboda Allah da fatar in samu lada daga gare Shi, sai ka yi yadda ka so da ita.”
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “A gaishe ka namiji! Ka kuwa samu gwaggwabar riba a wannan ciniki naka. Na ji abin da ka ce, amma ina ganin sai ka raba ta tsakanin danginka.” Haka kuwa ya yi! (Buhari da Muslim ne suka ruwaito Hadisin).
Shi sha’anin nan na zumunta yana yin naso ne har ya kai ga kyautatawa da girmama dangin-dangira, wato wadanda suke da kowane irin nisancin kusanci da wadanda ake dangantaka da su. Haka abin yake idan muka yi dubi da irin jan hankalin da Manzon Allah (SAW) ya yi wa sahabbansa kan su kyautata wa mutanen Masar, idan sun ci su da yaki, saboda surukutar da ke tsakaninsu, kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito.
Malamai sun fassara wannan al’amari da Hajara mahaifiyar Annabi Isma’il, (Amincin Allah ya tabbata gare su), da Mariya Al-kibdiyya, mahaifiyar Ibrahim dan Manzon Allah (SAW), wadanda dukansu biyun, sun fito ne daga Masar.
Madallah kuwa da irin wannan kyakkyawar dabi’a, wadda har wadansu na nesa ma suke samun alherinta, saboda haka ba abin mamaki ba ne a ga Musulmi na kwarai yana dokin ya ba danginsa hakkokinsu kamar yadda ya kamata, kuma ya kyautata musu.
Allah Ya tabbatar da duga-duganmu cikin wannan addini na Musulunci.
Za mu ci gaba