Tsokaci ga Shugaba Muhammadu Buhari (3)

Gaskiya ga dukkan alamu, ’yan Najeriya muna cikin rudani saboda rashin gane bambancin masaki da kwarya duk kuwa da yake ’yan uwan juna ne. Abubuwa da yawa suka sa na ce haka, domin mu ’yan Najeriya musamman ’yan Arewa mun tsinci kanmu cikin gaggawa kuma da saurin yanke hukunci koda abin zai kasance ba haka […]

Tsokaci ga Shugaba Muhammadu Buhari (3)

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Gaskiya ga dukkan alamu, ’yan Najeriya muna cikin rudani saboda rashin gane bambancin masaki da kwarya duk kuwa da yake ’yan uwan juna ne. Abubuwa da yawa suka sa na ce haka, domin mu ’yan Najeriya musamman ’yan Arewa mun tsinci kanmu cikin gaggawa kuma da saurin yanke hukunci koda abin zai kasance ba haka ba.

Da farko na san mu ne muke gaba wajen mara wa Shugaba Buhari baya tun shekarar 2003, kuma abin sha’awa a waccan shekara ya shigo siyasa tsindum, bayan rarrashinsa da wadansu dattijai suka yi ta yi domin suna ganin shi din “Good Material” ne, saboda kaunar da talakawa suke yi masa. Domin lokacin da Shugaba Buharin yakan fito cikin jama’a wato 1989-1997 za ka iske jama’a daruruwa sun zagaye shi domin kawai kauna wacce suke nuna wa Shugaba Muhammadu Buhari, wannan bayan ya yi mulkin soja a  1984-1985 inda daga karshe sojoji ’yan sa-ido suka ture waccan gwamnati da ta nuna kauna ga talakawan Najeriya.

Me Shugaba Buhari ya yi wa talakawa lokacin da ya yi mulkin soja a wancan lokaci? Gaskiya koda yake gwamnatin da aka ture siyasa ce kawai ta Kudu da Arewa, domin gwamnatin Alhaji Shehu Shagari, gwamnati ce da duk talakawan Najeriya suka ji dadinta domin babu wani abu da zai gagari talaka, tufa ce, abinci ne da kyakkyawar zamantakewa tsakanin kabilun Najeriya. Na taba zuwa Fatakwal a 1982, kuma na ga yadda kabilun can suka rika kyautata mana kuma dukkansu da hula irin yadda Shagari yake saka hularsa da babbar riga duk sun sa abin sha’awa. Kuma a lokacin NPN ita take da gwamnati a Jihar Ribas, saboda haka Gwamnan da kwamishinoninsa duk sun yi ado irin namu na Arewa. Ka ga koda yake shi Shugaba Buhari kirawo shi aka yi ya shugabanci kasa amma dai gaskiya “against his personal wish (sabanin son ransa).”

To, gaskiya Janar Buhari ya yi kokari ainun lokacin da ya hau mulkin soja a 1984 – 1985, wanda niyyarsa ta taimakon talakawa ce sai ’yan gaza-gani suka yi masa juyin mulkin da suka ce wai baya jin shawara abin da har gobe jama’a da yawa ba su yarda ba.

Kai dai ka san buhun shinkafa babba Naira saba’in (70.) ne, haka karamin buhun Semobita Naira biyar (5) ne, buhun sukari Naira talatin da biyar (35.) ne, Galan din man-toki (Turkey oil) kudinsa kalilan, wannan farkon tashin zabon shi ne ya sa jama’a masu yawa suka tabbatar Janar Buhari masoyin talakawa ne. Wannan shi ne dalilin da ya sa a shekarar 2003 ya zama zakaran gwajin dafi, muka tashi tsaye domin Shugaba Buhari ya dawo domin kyautata wa talakawan Najeriya wanda shi ne kullum batun masu mulki tun tale-tale.

Amma Allah cikin ikonSa, Shugaba Buhari bai samu mulkin ba sai a shekarar 2015, domin ya tsaya a shekarun 2003 da 2007 da 2011 amma da yake Allah Shi Ya san asirin boye sai a shekarar 2015 ya samu hayewa kuma yanzu 2019, ya sake darewa kan mulkin da yake yi wa lakabi da “Nes Labul” wato wai mataki na gaba.

A koyaushe burin masu mulki a samu kudaden tafiyar da gwamnati wadanda za a kashe wa ’yan majalisa da ministoci da kuma ita kanta fadar gwamnati da kuma tafiye-tafiye a jirgin sama wanda ba karamin kudi ake kashewa ta wannan balaguro na jami’an gwamnati a fadar gwamnati ba. Kamar yadda Shugaba Buhari ya je Rasha da Saudiyya wanda muke zaton wadannan kasashe ba da wasa suke ba ganin suna da karfin arziki ba kamar sauran kasashe ba wadanda sai dai kawai ’yan siyasar Najeriya masu handama da babakere su debi dukiyarmu su kai musu kudaden da har abada ba za su dawo Najeriya ba.

To, Shugaba Muhammadu Buhari gaskiya koda yake kana da masu farfaganda kusa da nesa da kai, ya zama dole a gaya maka gaskiya cewa a yi hanzarin bude iyakokinmu kuma a yi azamar haduwa da makwabtanmu domin su kiyaye mutuncinmu su kuma sa-ido a daina shigowa da miyagun abubuwa cikin kasarmu Najeriya. Su kuma masu shigo da kaya su dubi Allah su shigo da abubuwan kirki ba na cutar da kasa da talakawanta ba. Na san kasashe makwabta sun shiga tasku, tsorona kada su dauki matakin ramuwar gayya wacce ta fi gayya ciwo domin kowane allazi na da nasa amanu.

Kada a damu da kudaden da ake samu a dubi rayukan jama’a domin mai mulki yana can cikin ni’ima shi kuwa talaka ta me zai cika cikinsa yake yi. Gaskiya noma a cikin kasa yana kyau, amma koda Amurka da Rasha da Saudiyya ana shigo musu da shinkafa da alkama da sauransu. To yaya za a ce Najeriya ta sha bamban. Manoman Najeriya ku ji tsoron Allah, domin ku ta kanku kuke ba  ta talakawa ba. Shugaba Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya ka dubi Allah ka sauko kasa domin ganin yadda talaka ke shan wahala.

Kwamared Ibrahim Abdu Zango ya rubuto ne daga Kano, kuma za a iya samunsa ta: 08175472298