Tsokaci ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari

Ya zama dole mu yi tsokaci ga Shugaban Kasa Malam Muhammadu Buhari, saboda shi ne Shugaban Kasa tun shekarar 2015 zuwa 2019. Wannan dalili shi ne ya sa jama’a masu yawa suke ba da shawarwari da koke-kokensu. Hakika da yawa ba a daukar shawarwari, saboda watakila gwamnati ta fi damuwa da manyan kasa ko masu […]

Tsokaci ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari
Tsokaci ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari

Ya zama dole mu yi tsokaci ga Shugaban Kasa Malam Muhammadu Buhari, saboda shi ne Shugaban Kasa tun shekarar 2015 zuwa 2019. Wannan dalili shi ne ya sa jama’a masu yawa suke ba da shawarwari da koke-kokensu. Hakika da yawa ba a daukar shawarwari, saboda watakila gwamnati ta fi damuwa da manyan kasa ko masu ilimi wadanda yawanci su ne suke kewaye da gwamnati a kullum. Koyaushe kuma abubuwan da suke nuna wa gwamnati ba hakikanin abubuwan da suka shafi jama’ar kasar ba ne. Gaskiya Shugaba Muhammadu Buhari ya shigo cikin mulki lokacin da kasar nan ta shiga cikin wani mawuyacin hali duk da yake akwai jama’a da yawa da suke ganin wai jiya ta fi yau.

To wannan shi ne ra’ayin masu ganin haka domin a nufinsu shi ne ganin yadda komai yake kusan gagarar talakawa wanda yawancinsu su ne suke shiga rana domin zaben shugabannin da yanzu suke gasa wa talakawa aya a hannayensu.

Bayan da su Janar Babangida suka yi wa Buhari juyin mulki sun yi zargin cewa ba ya daukar shawara dalilan da jama’a da yawa ba su gamsu ba duk da yake koda lokacin da suka ture ko tunkude marigayi Alhaji Shehu Aliyu shagari (Allah Ya jikansa, amin), duk dan Najeriya hankalinsa a kwance yake bisa kyakkyawar rayuwa wacce duk duniya an tabbatar da haka domin duk wasu abubuwan rayuwa cikin sauki suke domin ana sayar da buhun shinkafa Naira 50 kacal, balle kudaden tafiye-tafiye dukkan lokunan Najeriya.

Gwamnatin Shugaba Shehu Aliyu Shagari gwamnati ce da ta sha suka wuraren da NPN ba ta da gwamnati kususan jihohin Kudu maso Yamma domin su ne suke da gidajen jaridu mafi yawa a Najeriya. Saboda haka kullum suka zauna ba su da abin yi, sai cin zarafin gwamnati duk mai ja da wannan magana tawa ya duba jaridun Kudu daga 1980-1984, zai fahimci yadda aka rika ragargazar gwamnatin wancan lokaci duk da tallafin da ’yan Najeriya suka sharba. Komai za ka ce dai sojoji sun yi kuskure sosai da suka yi wa waccan gwamnati juyin mulki wanda za a iya danganta wannan juyin mulki da wanda aka yi haka kurum a1966 wanda shi ne ya janyo rugujewar siyasa ta hakika a Najeriya. Shi kansa Muhammadu Buhari niyyarsa a 1983-1984 ya kyautata wa ’yan Najeriya inda su Babangida suka ture shi domin kawai suna so su ma su dana mulki, wanda sun yi kuma sun yi abin da suka yi ko dai na kyautata wa ’yan Najeriya ko kansu.

Abin sha’awa shi ne Janar Babangida yana nan muna fata Allah Ya kara masa lafiya da shi da dan uwansa Janar Abdussalami Abubakar wadanda suka fito daga gari daya kuma suka bar mulki ba tare da wata hayaniya ba, duk da zaben 1993 shi ne ya firgita Janar Babangida din barin mulki duk da ba haka ya so ba. To wannan dan karamin tsokaci na yi shi ne domin shi tarihi ba ya bata domin akwai masu inganta shi kafin wadansu su amsa kafin lokacin da sai buzun masu ba da shi.

To gaskiya Allah Ya kawo mu lokaci da ’yan Najeriya suka fi kokawa ganin bakar wahala da ake ciki kususan ganin yadda harkar tsaro take ciki duk da gwamnati tana iya kokarinta don shawo kan wadannan annobobi da suka addabar wurare kamar dai Arewa maso Gabas da ’yar uwarta Arewa maso Yamma kususan Katsina, Zamfara, Sakkwato har da Neja da sauransu.

Jama’ar Najeriya suna cikin halin ni-’yasu ganin ire-iren ra’ayoyin gwamnati bisa tsara tattalin arzikin kasa, abubuwan da yawancin jama’a suke ganin kawai domin tafiyar da gwamnati ne kususan masu mukaman siyasa daga kasa har sama wato tun daga kananan hukumomi 774 zuwa jihohi 36 da kuma ita kanta Abuja. Duk da yake dai ita gwamnati tana raba kudade ne ga kanta har jihohi da kananan hukumomi kuma ana yin haka ne don tafiyar da lamarinsu daga biyan albashi zuwa wasu abubuwa da yawa, to bayan Gwamnatin Tarayya ta yi haka akwai kuma aikin yau da kullum wanda duk dai lagwada ce da ke tattare da gwamnati da jama’arta wadanda ba talakawa ba ne.

A nan dai muna nufin cewa gwamnatin Malam Muhammadu Buhari ya zama wajibi a dubi talakawa sosai wannan lokaci saboda matsanancin hali da muke ciki kuma a yi hankali da ’yan gambara masu yabon gwamnati.Allah Ya kiyaye Najeriya, Amin.

Kwamared  Ibrahim Abdu Zango, Kano

08175472298