Tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna (2)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako. Bayan haka, yau mukalarmu za […]
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, yau mukalarmu za ta ci gaba ne daga inda:
Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya siffanta mana ita (hanyar zuwa shiga Aljanna din), a cikin fadinsa biyu: Farko ya ce, “Na bar ku a tsakiyar hanya, wadda take fara fat, darenta kamar yininta ne, (daidai yake, ko ta ina kyau gare ta). Ba wanda zai karkata daga kan wannan hanya, sai wanda yake batacce.”
Bayan nan ya ce, “Dukkanku za ku shiga Aljanna, sai wanda ya ki (ya ce ba ya so).”
Sai sahabbai suka tambaye shi, “Wa zai ki kuwa, ya ce ba ya son shiga Aljanna, ya Rasulallah?”
Sai ya ce, “Duk wanda ya yi mini biyayya, (ya bi abin da na karantar), ya shiga Aljanna; wanda kuwa ya saba mini, (wannan ya ce) ba ya son Aljanna (kawai, kai tsaye).”
Shi ya sa ya jama’a, ku ji tausayin wadanda suke cewa ba ruwansu da Sunnar Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda ba yadda za a yi mutum ya isa wurin Allah ba ta wurinsa ba. Domin yayin da aka aiko shi, duk wata hanya da za a bi don a kai wurin Allah ta wasu Manzanni, an toshe ta. Kamar a ce wuri ne mai kofofi daban-daban ta wurin shigar shi, to tunda aka turo Manzon Allah (SAW), aka kulle kofofin nan gaba daya, sai ta kofarsa ko hanyarsa kawai za a shiga wurin. Aka ce duk wanda yake so ya isa wurin Allah, ya samu rahama, sai ya biyo ta bayan Manzon Allah, Annabi Muhammad, (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Kai, hasali ma dai a Ranar Alkiyama su kansu jama’ar Annabawa, sai sun samu ceton Manzon Allah, (SAW), saboda shi za a ba “Shafa’atul Uzma” wato ceto madaukaki. Tashin farko, a filin Alkiyama, Allah Zai kyale mutane, a rika shan wahala, sai Manzon Allah ya je ya yi abin da Allah Ya so ya yi (na yabo), sannan Allah Tabaraka wa Ta’ala Zai saurari jama’a ma tukun –da su da Annabawan gaba daya.
Bayan an gama wannan, an yi hisabi, an gama abin da za a yi, akwai wata gada da ake hawa, bayan an hau siradi, sunanta kandara. Ita wannan kandarar, Annabawa ba su hawanta, sai dai wasu bayin Allah ne, (wato mu, insha Allah), sai wasu wadanda Allah kadai Ya sani, za mu hau ta. Duk wanda ya gan shi kan wannan gada, ya riga ya sha, ya tsira! Duk abin da zai kasance ya rage, sai dai kawai tsakanin ku ya ku. Watakila tsakanin kai da matarka, misali, akwai wasu ’yan abubuwa, (ko shi ma din) sai dai a ce, ‘A’a, ai an gama, tunda dai mun tsallaka, ai babu sauran wasu ’yan tone-tone.” Saboda a shiga Aljanna, babu mai sauran wata damuwa ko kullin zuciya a tare da shi, kamar yadda Allah Yake cewa, “Kuma Muka debe duk abin da ke cikin kirazansu (zukatansu) na gilli (kyashi ko kullin zuci), suka zama ’yan uwa a kan gadaje suna masu fuskantar juna.” (Suratul Hijr, aya ta 47).
Su Annabawa (AS), kamar yadda aka ce a baya, ba sa hawa wannan gada ta kandara, sai dai kawai a ga sun bullo a gabanta, saboda su Allah Ya zabe su, sun kasance zababbun bayin Allah. To, amma idan suka isa daidai kofar Aljanna, kowanensu an yi masa mumbari na zinari da zai hau ya tsaya, jama’arsa su zo wurinsa su taru.
Bayan sun gama taruwa, can kuma sai a ga Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bullo, sai kawai kallo ya koma kansa, wanda shi ma yana da munbarin da ya fi na kowa bisa, ta yadda idan ya hau mumbarin, yana ganin jama’ar kowane Annabi. Shi ma zai hau nasa mumbarin ya tsaya, iyakar yadda Allah Ya so.
Daga nan sai Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya sauko daga kan mumbarin, ba zai ce wa kowa komai ba, sai a bude masa wata kofa ya shiga. To, a nan ne zai kara zuwa gaban Allah ya fadi, ya karanta abin da zai karanta. Shi, Sallallahu Alaihi wasallam, ya ce, “Wadannan kalmomi da zan fadi, kafin ni ba a taba gaya wa wani su ba, ni ne farkon wanda aka ga gaya wa su, ni ne farkon wanda zai yabi Allah da kalmomin nan, kuma daga ni an gama har abada.”
To, lokacin da zai fadi wadannan kalmomin, zai fadi nan ya yi sujada, sai Allah Ya ce, “daga kanka ya Muhammad, ai yau ku bakiNa ne kawai, karrama ku ake, me kake so kuma, yanzu a yi?” Sai ya ce, “Ya Allah! Jama’a sun gama taruwa, ga Annabawa nan da jama’arsu, so nake yanzu a shiga Aljannar nan, Allah Ka ba da izini a shiga.” Sai Allah Ya ce, “An ba da izini. Da ma Na ce kada a bude ta, sai ka zo. Don haka je ka ce su bude.”
A lokacin da zai je ya yi magana, Mala’ikun da ke tsaron kofa za su ce “Wane ne kai?” Sai ya ce, “Ni ne Muhammad.” Sannan sai su ce, “Da ma an ce kada mu bude sai ka zo.” Daga nan za a bude Aljannar nan, sai Manzon Allah (SAW) ya juya wajen Annabawa ya ce, “Ku taho ya ’yan uwana ku shiga.”
To, kun ga ashe matsayin Manzon Allah (SAW) ba mai irinsa. Duk Annabawan nan suna nan, shi zai kira su su shiga Aljanna. Daga nan sai ya kira sahabbansa, wadanda su Allah Ya ba izini. Abubakar, (Allah Ya kara masa yarda), shi ne a gaba, sauran taran da aka yi wa bushara da shiga Aljanna suna biye.
Wani Abin Lura:
To, yau a ce mutum yana Musulunci, sannan ya ce ba ruwansa da abin da Manzon Allah ya koyar, ko kuma ya kasance wadannan sahabban nasa su yake zagi, yana la’antarsu (to mene ne Musuluncin nasa)? Kai, ban ga ta inda za a tsira ba, (in dai a kan haka ake) wallahi! Saboda haka ya jama’a, mu gode wa Allah da Ya sanya mu cikin al’ummar ManzonSa, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Wannan ba karamar daraja ba ce. Ba karamin matsayi ba ne. Kuma ba za a gane shi ba, sai an je can (Lahira)! Domin idan an je, ko a kira ka kawai a ce, “Ya kai (wane!) Cikin jama’ar Manzon Allah…” Kai ka san sauran al’ummomi sai sun kalle ka, saboda suna ganin cewa lallai wanda ya samu kansa cikin al’ummar nan ta Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya gama rabauta. To, amma yau ga mutum ya fitar da kansa (daga cikin wannan al’umma). Mutum ya ce ba ruwansa da abin da Manzon Allah (SAW) ya koyar, kawai shi iyakarsa Alkur’ani kadai? To, yaya za a yi ka gane Alkur’anin, alhali dan sakon da ya zo da Alkur’anin nan fa shi ne zai iya gane maganar Allah. Shi zai iya fadin abin da Allah ke nufi. In an zo wajen aiki, shi zai nuna yadda Allah ke so a yi aikin! Ka ce ba ruwanka da shi, to wa za ka bi? Yaya za a yi ka tsira da bin wanin Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam?
A gane, a fahimta cewa ita shari’ar nan ka’ida ce, an gina ta a kan abubuwa biyu kacal: (1) Yi don Allah kadai (ikhlasi) da (2) Kwaikwayon Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Mu kwana nan.