Tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna (6)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (SAW), tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako. Bayan haka, muna nan […]
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (SAW), tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, muna nan dai a kan hanyarmu ta zuwa Aljanna. Muna karkashin kashi na biyu na tafiyar, wanda ya kunshi ayyuka na kwarai bayan imani, inda muka kwana bayan mun yi bayanin tsayar da Sallah. Yau ga ci gaba daga kan:
2. Mu ba da zakkar dukiyarmu idan akwai, zuwa ga wadanda aka ce mu ba su na daga cikin mutum takwas din da suka cancanci cin zakkar! Wato abin sani kawai shi ne dukiyoyin sadaka (zakkah) na fakirai ne da miskinai da masu aiki a kansu (ma’aikatan zakkar –wato masu karba su rarraba ga wadanda suka cancanta) da wadanda ake lallashin zukatansu da kuma a cikin fansar wuyoyi (’yanto bayi Musulmi) da wadanda bashi ya cukuikuye su da kuma cikin hanyar Allah (duk abin da zai taimaka wajen daukaka matsayin Musulunci –na daga jihadi da da’awa da karantarwa da sauransu) da dan hanya (matafiyin da guzurinsa ya yanke, a ba shi koda shi a garinsu mawadaci ne). Farilla ke nan daga Allah! Kuma Allah ne Masani, Mai hikima! (Suratu Tauba –aya ta 60). Wadannan su ne mutane takwas da Allah Ya ce a raba wa zakkah.
Wajen bayar da zakkar, lallai ne mu ga cewa abin da za mu bayar mai kyau ne. In zakkar noma ce mu bayar da mai kyau, kada mu duba mara kyau mu ce shi za mu bayar. Misali a duba marasa kwari, a ce, “Bari mu cire da cikin wannan mu bayar.” Me ya sa za ka ba Allah abin da kai in da za a ba ka ba ka so? Ka ga ke nan wannan ba daidai ba ne. Saboda haka, sai mu cire mai kyau kammalalle mu bayar. Bayan nan, babban aiki a cikin – ikhlasi – wato mu yi don Allah kadai da neman yardarSa. Wajen bayarwar, kada a ba da ana gori ko ana gintse fuska – kawai a sanya a rai kuma fuska ta nuna cewa an yi abin ne don Allah kadai – wato an nuna godiya ga Allah, Wanda Shi ne Ya bayar da wannan dukiya, kuma an cire hakkin da (Allah din) Ya wajabta a bayar daga dukiyar.
3. Mu yi azuminmu (na Ramadan) muna masu kamewa daga duk abubuwan da ke karya azumin nan, kuma mu kiyayi abubuwa mutashabihatu (masu rikici) da abin da yake haramtacce a cikin zantuttukanmu da ayyukanmu. Kada ka kai azuminka lafiya lau, amma ka zo wajen yin buda baki ka yi da abin da yake haram. Ka kwakulo kayan wani, misali ka ce, ai sai ka ci kaza kai ma! A’a, abin da Allah Ya hore maka ka yi hakuri da shi, ka yi buda bakinka da shi. Abin da yake da muhimmanci dai shi ne fatar Allah Ya karbi azumin.
Lallai mu kiyaye al’amarin azumi a cikin zantukanmu da ayyukanmu. Mu rika fadin maganganu masu kyau; a ayyukan kuma mu dage wajen aikata masu kyau su ma. Haka tunaninmu lallai kada mu rika mummunan tunani game da Allah, ga shi muna azumi; mu kyautata manufofinmu dangane da duk ayyukan ibada da muke yi. Kamar yadda ya gabata, mu maida hankali wajen gudanar da duk ayyukan nan saboda Allah kadai da neman yardarSa!
4. Mu yi Hajji! Mu samu a rayuwarmu, mu je aikin Hajji mu gudanar da shi kamar yadda Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi nasa hajjin. Mu samu a rayuwarmu mu je dakin Allah, mu yi aiki karbabbe. Aiki ne da za mu yi, wanda ya kubuta daga abin da bai kamata ba, kamar kusantar iyali da fasikanci da rafas (kwarkwasa da duk abin da zai bata shi) da jidali (jayayya), kuma ya kasance wanda aka cika shi da ayyuka na alheri masu yawa. Maimakon ka je karbar sabil (kayan da ake bayarwa sadaka ko kyauta), sai ya kasance kai ne ke bayar da sabil din. Maimakon ka karbi sadaka, ya kasance kai ne ke bayar da sadaka. Maimakon a dauki nauyinka, kai ne kake daukar nauyin wasu, ka zamo kana gudanar da alherai ta kowace fuska. Saboda duk wanda ya ciyar a Makkah, ba kamar wanda ya ciyar a garinsu ba ne, domin a can bakin Mai Rahama ka ciyar. Saboda haka kada ka kasance ga guzurinka ka kulle kana karbar kayayyakin da suke bayarwa a can kana ci, har ma kila ka rika tunani kana cewa, su dolaye ne! To, in ka yi haka, lallai kai ne babban dolon! Mai kokarin ka ci kayan wani, kai hannunka ya zama kasa (mai karba), ba sama (mai bayarwa) ba.
Ka yi kokari ya kasance ka gudanar da ayyukan alheri ta kowane fanni don ka samu abin da ake bukatar a kai gare shi na samun kubutaccen Hajji!
Malam Aljaza’iriy, a ci gaba da nuni kan irin sinadaran da ake bukata a wannan tafiya, a kan hayar zuwa Aljanna, ya ce:
1. Sannan mu yi wa iyayenmu da’a! Mu yi kokari duk abin da yake na kyautatawa mu yi musu, suna raye ne ko a’a. In suna raye, mu yi musu du’a’i, mu yi musu duk abubuwa da suke bukata na rayuwa; wato abin da ya danganci tufatarwa da ciyarwa da shayarwa da duk wani abu da ya jibinci girmamawa gare su. Bayan sun mutu kuma koyaushe kada mu manta da su cikin addu’o’inmu. In za mu yi wasu ayyukan alheri kamar sadakoki, mu rika bayarwa da niyyar muna yin sadakar ne don su amfana, mu da su. In an yi haka, to an bar ’ya’ya nagari ke nan, wadanda iyayensu za su rika murna da su a inda suke kwance a barzahu! In kuwa aka samu akasi, Allah Ya kiyaye, to iyayen mutum kullum sai sun yi kuka! Saboda haka mutum ya yi kokari ya kyautata musu, suna raye da bayan sun bar duniya. In an yi haka, to an kama hanya ta shiga wannan gida na morewa da jin dadin rayuwa, wadda ba ta yankewa.
Ita da’ar nan da za a yi wa iyaye, to a yi ta ba cikin abin da yake na sabon Allah ba. A yi musu ihsani (kyauta-yi), wanda ya dace da shari’a na aiki da magana, alhali ana kallo yanayin yadda ake kyautata musu din, su yi murna da farin ciki da abin da aka yi musu. Abin da su suke so suke bukatarsa, shi ne za a yi musu, ba abin da kai kake ganin shi ya fi dacewa da su ba. Lallai dai kowa ya san abin da zai yi wa mahaifansa su ji dadi; abin da za ka yi wa mahaifanka su ji dadi, wani in ya yi wa nasa mahaifan, ba lallai ne su ji dadin hakan ba. To, kowa sai ya kalli yanayin nasa mahaifan, ta fuskar abin da ake musu su ji dadi. Misali in lokacin sanyi ne, a ga me suka fi bukata a yi musu; in lokacin zafi ne, a duba a ga me suke bukata; a lura da yanayi da wuri da ma shekaru.
Mu kwana nan!