Tsokaci, kalubale da al’amuran dubawa dangane da sake fasalin Najeriya (I)
An samu lokaci mai tsawo, masana da ma gama-garin mutane suna ta kai-kawo game da batun sake fasalin Najeriya. Dangane da wannan batu, kwararre kan al’amuran mulki, masanin al’adu da zamantakewar al’umma, marubuci, DOKTA BUKAR USMAN OON ya yi nazari, sannan ya gabatar da bunkassashen tsokaci, kamar haka: Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 […]
An samu lokaci mai tsawo, masana da ma gama-garin mutane suna ta kai-kawo game da batun sake fasalin Najeriya. Dangane da wannan batu, kwararre kan al’amuran mulki, masanin al’adu da zamantakewar al’umma, marubuci, DOKTA BUKAR USMAN OON ya yi nazari, sannan ya gabatar da bunkassashen tsokaci, kamar haka:
Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), yana kunshe da tanade-tanaden da ake bukatar bi a duk lokacin da ake son canja shi ko kuma yi masa kwaskwarima. Irin wadannan tanade-tanade, akwai su a cikin kundayen da suka gabaci wannan. Sai dai kuma ka’idoji da tanade-tanaden suna da matukar sarkakiya da fadi. Wadanda suka tsara kundin, sun yi haka ne da sani, musamman domin a dakile kofar saka wasu al’amura marasa amfani, domin a tabbatar da hadin kan Najeriya.
A lokacin da ake kiraye-kirayen sake fasalin Najeriya, ke nan ana kira ne da a sake fasalin wasu sassa ko dukkan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999. Sarkakiyar da ke tattare da tanade-tanaden da ke kunshe a kundin, su suka sanya wasu mutane ke kokarin yi masa karan-tsaye, inda wasu ma ke kushe shi cewa bai dace da tsarin dimokuradiyya ba. Wasu ma sun nuna bukatar cewa ya kamata a canja kundin gaba daya, domin a cewarsu ya dace da “tanadin damakaradiyya.”
Babu ko shakka, masu kwarmato da kiran sake fasalin kasa kalilan ne kuma sun kasance a wani bangare na kasar nan. Amma duk da haka, wasunsu fitattu ne da ake darajawa a cikin al’umma, wadanda suka kasance hamshakan ’yan siyasa, ma’aikatan gwamnati, malaman jami’a, lauyoyi, malaman addini, sarakunan gargajiya da tsofaffin jami’an tsaro da sauransu. Wadansunsu sun taba rike mukamai a gwamnati, wasu ma har yanzu suna kan aiki, wasu kuwa ba su ma taba rike wani mukami ba. Haka kuma akwai ma wadanda kawai ’yan kwarmato ne, na-zaune-ne-gwanayen-kallon-kokowa, wadanda ma ba su san dawan garin ba. Wasu kuwa a iya cewa Allah-san-barka, sun san abin da suke yi, suna da kyakkyawar manufa ga al’umma, don haka ba za a zarge su da son kai ko don neman abin duniya ba. Sai dai kuma ba za ka raba daya biyu ba, masu kwarmaton sake fasalin kasa, za a iya gani karara cewa suna kambama manufa ce ta bangaranci, wacce daga karshe za ta iya lalata turakun hadin kan kasa. Wasunsu za ka ga suna kambama ra’ayinsu da dukkan karfin da suka mallaka, wasu ma har da yin barazanar haddasa fitintinu ga kasa, idan har son zuciyarsu bai samu biyan bukata ba a lokacin da suka gindaya, alhali sun mance ko kuma ba su gane cewa shi gina kasa wani al’amari ne mai gudana, wanda ba a son yi masa tsaiko.
Haka kuma, wasu ma sun bi yarima ne kawai domin su sha kida, alhali ba su san dawan garin ba, ba su sam kalubalen da ke tattare da batun sake fasalin kasa ba. Wannan ne ya tuna mani da wani al’amari da ya taba faruwa a lokacin mulkin Gowon, yadda wasu dalibai suka hau titi suna zanga-zanga, suna kwakwazon cewa: “Dole Ali Ya Tafi!” Kan haka, wadansu ma da ba daliban makaranta ba, suka shiga cikinsu, su ma suna ta kiran “Dole Ali Ya Tafi!” ba tare da sanin hakikanin dalilin zanga-zangar ba. Haka fa al’amuran Najeriya suka rika gudana da korafe-korafe iri-iri, na kirki da wadanda ma ba na kirki ba.
Na nazarci bayanan wasu daga cikin masu neman a sake fasalin Najeriya, inda na gano cewa suna nuna rashin gamsuwarsu ne na yadda ake tafiyar da mulkin kasa. Suna nuna rashin gamsuwa ta fuskar rashin daidaito a Gwamnatin Tarayya, musamman ta fuskar rarraba mukamai da kuma arzikin kasa. Haka kuma suna ganin cewar ana tafiyar da gwamnati ne a tsarin Hada-Ka, maimakon tsarin Fadaraliyya da suke bukata.
Abin tambaya a nan shi ne, shin ina mafita ga wannan kwakwazo da tada-jijiyar-wuya da ake yi game da sake fasalin Najeriya?
Wasu masu son a sake fasalin Najeriya sun nuna bukatar a koma wa Kundin Tsarin Mulki na 1963. Sun kafa hujjar cewa wannan kundi ne kadai a tarihin Najeriya da fitattun ’yan siyasarmu na dauri suka shirya, bayan sun yi zurfin tunani da tattaunawa sosai a kansa. Larduna uku (da suka koma hudu daga baya) da aka kirkiro a karkashin wannan Kundin Tsarin Mulki, sun biya bukata sosai wajen bunkasa kasa bisa jagorancin siyasa. Babu shakka an samu ci gaban al’umma sosai a wadannan larduna, cikin kankanen lokacin da suka kasance.
Masu kare batun fasalin kasa kuma sun bayyana cewa baya ga wancan Kundin Tsarin Mulki na 1963, dukkan wadanda suka biyo bayansa, sojoji ne suka samar da su. Har ma suka kafa misali da Kundin Tsarin Mulkin 1999, wanda a halin yanzu ake amfani da shi, cewa Gwamnatin Mulkin Soja ce ta samar da shi. Don haka suke kokarin ganin cewa lallai an canja shi, yadda zai dace da tsarin mulkin “Fadaraliyya-Hakika” ta kowane janibi. Suna bukatar tsarin da zai yi kamanceceniya da wanda ake da shi a shekarun 1960, wanda ya tanadar wa larduna isassar dukiyar da ta taimaka masu suka gudanar da gagaruman ayyuka. Sai dai kuma masu irin wannan tunanin, sun kasa gane cewa a yanzu, irin dimbin kudaden da jihohin yanzu 36 suke samu, sun fi wadanda lardunan baya suka samu.
Bari mu kara yin wata tambaya, shin wadanne dalilai ne suka sanya Najeriya ta yi watsi da tsohon Tsarin Lardi-Lardi da ya gudana a shekarun 1960, in dai har ana ikirarin cewa ya yi nasara?
Mutane na da mantuwa, domin kuwa wasu sun manta da cewa a can baya, irin wadannan korafe-korafe da kiraye-kiraye ne suka haddasa har aka karkatsa Najeriya zuwa jihohi, domin a share masu hawayensu na cewa ana kwararsu, matakin da ake ganin cewa da ba a dauke shi ba, yana iya kashe kasar gaba daya. A lokacin, ganin cewa ba a jima da samun ’yancin kan kasa ba, masu kishin kasa sun tsaya kai da fata, cewa bai kamata su bari a samu rarrabuwar kai ba, don haka suka danne bukatun kashin kansu, suka samar da hadin kan kasa.
Za mu ci gaba