Tsoma jama’a a harkar kudi: Yadda bankuna ke jan ra’ayin wadanda ba sa harka da banki

Tsoma jama’a a harkar kudi wani shiri ne na samar da tsarin mu’amala da kudi mai inganci kamar ajiya da bashi da inshora da fansho da suke da amfani da dacewa wanda aka tanada don daukacin jama’a musamman masu karamin karfi. Amfanin tsoma jama’a a harkar kudi ga talaka na da matukar muhimmanci. Wannan tsari […]

Tsoma jama’a a harkar kudi: Yadda bankuna ke jan ra’ayin wadanda ba sa harka da banki

Tsoma jama’a a harkar kudi wani shiri ne na samar da tsarin mu’amala da kudi mai inganci kamar ajiya da bashi da inshora da fansho da suke da amfani da dacewa wanda aka tanada don daukacin jama’a musamman masu karamin karfi.

Amfanin tsoma jama’a a harkar kudi ga talaka na da matukar muhimmanci. Wannan tsari ba wai kawai yana kawo bunkasa ba ne har yana magance rugujewar tattalin arzikin iyalai. Wani bincike da Cibiyar Samar da Hada-Hadar Kudi (EFInA) ta gudanar a Najeriya a shekarar 2016 ya nuna mutum miliyan 40.1 wandanda suke wakiltar kashi 41.6 cikin 100 na adadin mutanen da ba sa hada-hadar kudi da bankuna, mutum miliyan 36.9  ne kacal suke mu’amala da banki wato suke da asusun ajiya a bankuna wanda hakan ke wakiltar kashi 38.3 na adadin mutanen da suka balaga a kasar baki daya.

Cibiyar EFInA ta bayyana cewa shigar jama’a musamman wadanda ba sa mu’amala da bankuna kwata-kwata da wadanda ba su damu da yin mu’amala da banki ba cikin harkar kudi  ya taimaka wa tattalin arzikin da cire kudi daga bangaren da ba ya cikin tsari zuwa bangaren hada-hadar kudi da ke kan tsari.

Binciken Cibiyar EFInA na shekarar 2016 ya nuna cewa mutum miliyan 23.9 ne kacal suka ajiye kudinsu a gida. Idan da a ce kashi 50 daga cikin 100  na wadannan mutane suna ajiye Naira dubu daya a wata a banki, da fiye da kimanin Naira biliyan 143 za a iya sanyawa a bangaren hada-hadar kudin mai tsari duk shekara.

Saboda muhimamancin haka ne ya sanya Babban Bankin Najeriya (CBN) da bankunan ajiyar kudi da Hukumar Daidaita Harkokin Bankuna ta Najeriya da Kungiyar Masu Hada-hadar Kudi na Tafi-da-gidanka masu lasisi da Dillalan Hannun Jari suka hadu a karkashin shirin SANEF wato Dillalan Fadada Hannun Jari don gaggauta  sanya mutum miliyan 40 masu karamin karfi da wadanda ba su ajiya a bankunan Najeriya cikin tsarin tsoma jama’a a hada-hadar kudi.

Tsarin yana son cimma kara kaiwa ga cin moriyar kudi daga dubu 50 zuwa dubu 500 a shekarar 2020 tare da zurfafa samun damar cin moriyar hada-hadar kudi daban-daban ta hanyar tafi-da-gidanka da ta Intanet da dama iri-iri kamar mallakar asusun ajiyar kudi da kananan basussuka da inshora da fansho ga ’yan Najeriya.

Me ya sa tsarin SANEF ke da muhimmanci?

Kamar yadda kafar bincike da kididdiga ta duniya ta nuna dangane da tsoma jama’a a hada-hadar kudi a duniya da  shiga cikin hada-hadar tsarin kudi, shirin na fitar da talakawa da marasa galihu daga cikin tsananin  talauci kuma yana rage bambancin da ke tsakanin al’umma. Tsoma jama’a a harkar hada-hadar kudi ta bankuna ba kawai tana taimaka wa daidaikun mutane da iyalai ba ne har yana bunkasa al’umma baki daya kuma yana taimakawa wajen karuwar tattalin arziki da kuma taimaka wa jama’a wajen samun damar tafiyarwa tare da ajiye kudinsu da bunkasa jama’a da samar da dabaru da ilimi ta yadda za su samu damar yanke shawarwari dangane da kudinsu. Rahoton ya nuna cewa shiga  adama a harkar banki mai tsari yana kai daidaikun mutane su amfana da abubuwa masu yawa da suka hada da:

– Samun damar farawa da bunkasa kasuwanci wanda zai bai wa jama’a dama ta hanyar tsarin hada-hadar kudi misali iya hasashe mai kyau na tsawon lokaci.

– Iya biyan kudin makarantar yara wanda hakan zai sanya al’ummar da za su zo nan gaba su zama masu ilimi da wayewa.

-Iya magance kalubale da ke bukatar biyan kudi na gaggawa da matsalar da ba a zata ba ko matsalar kudi na auke.

Me ya sa bankuna suke aiwatar da tsarin?

Har lokacin fitowar wannan rahoto sababbin dama a fannin kudi dubu 70 aka bullo da su zuwa yanzu tare da adadin da ake so a cimma na dubu 150 a karshen bana. Kamfanoni tara ne a yanzu suka shiga tsarin kudi na SANEF inda tuni aka raba Naira biliyan hudu da rabi.

Tsarin SANEF  ya himmatu wajen kara adadin da ake dashi na mutum miliyan 33 da ke da lambar ajiya a banki ta BBN zuwa mutum miliyan 70 a shekarar 2020.

Tuni aka raba kananan na’urorin rajistar lambar ajiya ta BBN dubu 10 da Cibiyar NIBSS ta samar ga bankuna da dillalai da aka sanya su yi wa mutane miliyan 10 rajistar lambar BBN a shekarar 2018 da mutum miliyan 15 a shekarar 2019 da kuma mutum miliyan 15 a shekarar 2020.

Cibiyar NIBSS za ta samar da kananan na’urorin yin rajistar ga dillalan da suke kasa baki daya musamman ma wadanda suke kauyuka kamar a Arewa maso gabas da Arewa ta tsakiya da Arewa maso yamma. NIBSS za ta biya Naira 100 ga duk ma’aikatan da suka yi rajistar lambar BBN din da suka yi.

Daya daga cikin ’yan Kwamitin Tsare-tsare na Kwamitin Bankuna  kan tsarin SANEF, Bolaji Lawal ya ce za a tura jami’an zuwa kananan hukumomi 774 da cibiyoyin kamfanonin sadarwa da kasuwanni.

Ya kara da cewa “An tsara adadin da ake so a bunkasa daga dubu 100 zuwa dubu 150 na zango na uku da na hudu na shekarar 2018. Tuni aka fara bayar da horo da takardun shaida da tsare-tsaren yadda za a fara aikin nan ba da dadewa ba da wayar da kan jama’a kan hada-hadar kudi da wayar da kan abokin hulda wanda za a gudanar a kafafen yada labarai da jaridu.

Da yake karin bayani kan shirin, Babban Jami’an Gudanarwa na bankin Diamond Bank, Uzoma Dozie ya ce “Batun samar da shaida wata matsala ce ta rashin samun daidaito da zubewar  kimar tsarin. Bangaren bankuna sun ce mutum miliyan 35 ne kacal ke yin hada-hada da su wanda hakan ya yi karanci kwarai da gaske idan aka kwatanta yawan al’ummar kasar nan. Bankuna sun tattaru karkashin tsarin SANEF kuma babbar manufar tsarin SANEF shi ne a rushe tsarin dillanci bankuna ta yadda kowa zai iya yin mu’amala da kowane banki.

Da yake karin haske dangane da cimma burin da ake so a cimma ya ce “ Wannan lamari zai kawo sauyi zuwa gaba idan gwamnati ta fito ta ce duk mu’amalar kudin da ta zarta Naira dubu 100 dole ta zama ta na’ura za ka ga abin da zai faru. Nan take za ga mutane sun fara bude asusun ajiya. Idan ka rage shi zuwa dubu 50 za ka ga mutane suna gaggawar shiga cikin tsarin idan kuwa ka rage zuwa Naira 10 za ka samu adadin mutane masu yawa da suka shiga tsarin. Dalilin da ya sa mutane suka da asusu ajiya a Ingila shi ne ba zai yi wu ka rika daukar tsabar kudi ba saboda tsadar yin hakan ke da shi, masu hada-hadar miyagun kwayoyi ne kawai ko kuma mutanen da ke son kaucewa haraji ke yin haka. Dalilin da ya sa suke daukan tsabar kudi shi ne don  rage yawan harajin da za su biya”.

Lawal ya karkare da bayyana cewa “Dabarar da ke cikin tsarin ita ce tabbacin samun cimma burin da aka sanya tare da kawo muhimmin sauyi a tsarin hada-hadar kudi ta baidaya da zabar hada-hadar banki ta yanar gizo tare da rage yawan wadanda ba sa mu’amala da banki.

“Zai rage iyakar bayar da bashi ga daidaikun jama’a da masu kananan sana’o’i da sanya kasuwancin da ba ya cikin tsari cikin tattalin arziki da walwalar jama’a,” inji shi.