Tsomomuwar tsiron tsoron tsaro (1)

Lado da Okonko da Lasisi Kun tara taro da sisi Ko ba ku da ko asi Ku kwankwadi kulara ta zarce fifsi Ku daina wasi-wasi   Lumana nai muku sammatsi Rakitar rigingimun uwar watsi Na kwadin makwalwarku na dada zartsi Har an shiga halin matsi Ana ta tsi-tsi   Gutsire-gutsiren gaftarar gautsi Ga gurin guntsi […]

Tsomomuwar tsiron tsoron tsaro (1)

Lado da Okonko da Lasisi

Kun tara taro da sisi

Ko ba ku da ko asi

Ku kwankwadi kulara ta zarce fifsi

Ku daina wasi-wasi

 

Lumana nai muku sammatsi

Rakitar rigingimun uwar watsi

Na kwadin makwalwarku na dada zartsi

Har an shiga halin matsi

Ana ta tsi-tsi

 

Gutsire-gutsiren gaftarar gautsi

Ga gurin guntsi

Dasashi durfafar dashishi yai santsi

Hakora na ta motsi

Tauna tantakwashin dutsi

 

Datsar dawar datsi

Tutsun tumbatsar tutsi

Kotson kidan kotsi

Katse-katsen karktsa katsi

Yakice-yakicen yamutsi

 

Hatsaniyar  hantsewar hantsi

Hayaniyar hadidiyar hatsi

Katobarar kassara kimtsi

Lotse-lotsen lallaga latsi

Rumuts-rumuts rumurmutsar rotsi

 

Kun dai ji kwaramniyar kirdi

Ga gadarar gardamar gardi

Kulle-kullen kulla kaidi

Daga-dagar dadin dannawa dandi

Kashe-kashen kasafta karatun kundi

 

Kwaramniyar kwaram da kwamdi

Kwakwazon kurda-kurdar katantawar kadi

Kai-kawon kewayen kodi

Kuntukun kalangun kidi

Karime-karimen kalimo kudi

 

Cukurkudewar cukudi-cukudi

Tambadar tunzurar turo tumbudi

Razanar rakin radadi

Raurawar rangajin rudi

Ziryar zirga-zirgar zakwadi

 

Rai kan ga rai

Rairaye rairayin rai-rai

Fuffukar fatattakar fakirai

Tereren tunkuyin takarkarai

Turnukun tataburzar takadarai

 

Makircin makirai

Mahaukata masu makarai

Kwakwar kwari kwarai-kwarai

Birgimar basajan birai

Salallamin Salamatu sarai-sarai

 

Wasu na ta kus-kus

Bibiyar batutuwa cunkus

Jikkata jikkuna jama’a lilis

Taron tattare tari tatas

Wawar wafciya warwas

 

Masu maganganu mukus

A taho-mu-gama an yi ragas

Na-zomon ingarma ko canjaras

Korar kaza ne as-as

Ashe ba cas ba as

 

Masu son bati

Na ta daga sauti

A baje nama su yanka da balati

Sun zaburo da karfin karti

Gumurzun gwankin gwabje gwamnati

 

Wasan Samson siya-siya

Dama-damar kurdiya

Siyasar tsiwar tsiya-tsiya

Dogogwaragon danboton tsautsayin tsintsiya

Dundumin dama-damar damon-kurar-diyya

 

Solle tagiya ya tsula dare

Ba batun Ba’are

Kowa yana ta yarfen yare

Wukaken magabta na nan zare

Mun gaza yunkurin kariya a tare

 

Kumajin kin ji kiris

Karshen tasuniya ne kururungus

Ana sane da masu yi mana algus

Masu cumuimiyar cin cukubus

Da camamar cukuikuye ca’ammas

 

Macuta mamuguntan macizan muzurai

Tsittsigen tsige-tsigen tsige tsirrai

Tantagarayar tashintashina tarai-tarai

Sare-sarin sare-saren sakarai

Sakarcin sakacin susucewar sarai

 

Ana ta artabu

An gaza garkame gambu

Dumuiniyar dasashin dakumar dambu

Rugugin ruftawar rufin rumbu

Ana ta ayyukan ayyana aibu

 

Mamungar majigi

Mutane  masu magagi

Kafafar karf-karfan kwanji

Kiriniyar kin ji

Kundumbalar kakalen kugi

 

An yi gaba-da-gaba

Ana ta gaba da giba

An jefa al’umma ukuba

’Ya’yan Inna da Baba

Wasu sun zam ’ya’yan dabba

 

Hakilon hankoro

Torokon toro

Bobon burgar bambaron Bararo

Kakarin kiraye-kirayen karo-karo

Wariyar warware awarwaro

 

Ina masu kishin tarayya

Ai taron tarairaya

Kowa ya bi bi-da-bin biyayya

Ban da kiren kanzon kuregen kurya

Mui magantuwar manufar murya

 

Kasa ta birkice

Al’amura sun rikice

Ana ta ka-ce-na-ce

Har ma da ce-ce-ku-ce

Zaman zaurukan zaurance

 

Tsomomuwa tsagwaro

Tsinkayen tsinin tsiro

Tsananin tsoro

Tsare-tsaren tsaro

Tsince-tsincen tsingaro

 

Ga garin gyauro

Maiwar Mowar accar acicin iburo

Borin Borar bigi bagiro

Damar damun daurin dauro

Gasarar gudajin garin gero

 

Limbu-limbun lafkewar loko

Kasurgumin kakkarfan kato

Karfa-karfan kunduge koto

Kosan koshin koshiyar kulunboto

Kullin kullun Karin kumallon koko

 

Jarumtar jimirin jelen Jauro

Bambamin bakin bubbuga bambaro

Kwaramniyar kwanaren kwararo

Zagayen zungurun zanzaro

Kakare-kakaren kiren kankaro

 

Bare-baren bare bauren bangaro

Kankamewar kankanen karo

Jimurdar jirgin dankaro

Murjin mazari zaro-zaro

Zirin zaren ziryar zizaro

 

Babban birnin Bararon-nono

Amincin Alanguburon Afuno

Tsautsayin tsukukun tsugunno

Bambance bobon bokokon bonono

Garkame gambun ginin ganuwar gano

 

Damuwar Dama-tumatur

Kwallon kurungu da hura usur

Farautar farmaki fafur

Bilinbituwar buga baburido bur

Take-taken tattakin take totur tur

 

An ji jiki a Jihar Yawon-Bebe

Mutane na yunkurin tashin babe

Don gudun masu wuka a kwabe

Ana ta kwarara kowane gwadabe

Asabarin Asabe an sassabe

 

Zogin zaman fargabar fara

Zama ne na daura damara

Barayin bisashe na hantara

Lullumin lumana ya gagara

Mummunan hali ya sa an gundura

 

Kudun kadadar kadawa

Ana ambaliyar aman-teku

Tsarin tsaron tsukuku

Tsokacin tsoron tsurku

Halin Haurobiyawa

 

Shaguben shaggun kafa kusa

Fankamar fitimu a fasa

Kar ai fashe-fashe a farfasa

Kaskacin kasa yai kasa-kasa

An daina wasa balle a warwasa

 

Hayaniya tai yawa

Ga tsugugidin ’yan yawa

Tsangwama ba kakautawa

Miyagu na ta shewa

Tsilla-tsillar tsawwalar tsurewa

 

Mabiya addinai

Sun tara taro da nai

Suna ta haushin karnai

Jama’a an toshe musu gannai

Ba masu magannai

 

An samu masu safarar  makamai

Don tada husumar rashin mukamai

An tabbatar mini akwai limamai

Sun karbe matsabban hannun jarmai

Za su tara masa jarumai

 

Masifu sun maishe da garuruwa kufai

An dai baje bayanai a faifai

Mu daina taku lakaikai

Fitintinu sun zamo alakakai

A wangale na-mujiyar ganin geffai

 

Baraden bindiga

Bar zari-ruga

Ko harbi ba jan daga

Miyagu sun rududduge ruga

A birane an kakkarya katanga

 

Masu dangar jinka

An yi muku aika-aika

Sace-sace sakaka

Kashe-kashen kiki-kaka

Garkuwar kuwwar rani da kaka

 

Wannan lamari

Aika-aikar bata-gari

Na jefa jama’a garari

A zabura ai hanzari

Ai wa baragurbi tarnakin tokari

 

Manyan masu fashi da mukami

Su ke haifar da fushin fashin da makami

Talaka na sha miya lami

An jefa jama’a jimami

’Yan tsirari sun wawushe burgami

 

An durfafi dazuka

A lalubo jaruman baka

Wadanda za su raya su daka

Ko’ina su afka

Zuwa mazaunin masu munin tufka

 

A yasar da jifan jarfa

Lumana tai kamfa

Ai hadakar kyakkayawar manufa

Ta zam an wassafa

Aiki a aikace kar a kikkifa

 

Nawar nau’ukan na’urori

Nauyayya niyar ninkayar shiri

Kokowar kakkabe sharri

A tunkari masu kawo hari

A tsawatar musu su bari

 

Dole dai a sake shiri

A bar batun masu sihiri

Al’umma a kara kokari

A yasar da mummunan kuduri

Mu dai zam jama’ar jajircewar jimiri

 

Bin kadin ilahirin al’umma

A kididdige alkaluma

Jidalin jaddawalin malumma

Manufar mutane masu himma

Kasa ta zam ta samu makama

 

Alaramman almajirai

Alhajin attajirai

Furkaniyar fitinar fakirin fakirai

Jinjina jiniyar jinjiniyar jarirai

Juwa-juwar ja-in-jar ja’irai

 

A dai yi kaffa-kaffa

Turakun tsaro a kakkafa

Gobara a samo ruwa a yayyafa

A samu kura ta lafa

Mui musafiha mu tafa

 

Arewatawa

Ai kawancen karfafa gwiwa

Ai wa magabta kawanya

A sasanta matuka gaya

A daina gogoriyon kokoyin wawa

 

Kadadar kadawa

Kandamar kadan ruwa

Kakarin kamun kurwa

Kadarkon dakon dagar dawa

Kui kama-kama kowa-da-kowa

 

Tsoho da tsohuwa

Bako da bakuwa

Ku daina kuwwa

Ku dai ba da gudunmuwa

Mui tinkahon takun tururuwa

 

Mu dora sanwar murhu

Mu daina rakin ihu

Don rashin taro da ahu

Ga gararumar garkar gayaunar dinke buhu

A ci tuwo da miyar taushen alayyahu

 

Masu fuka-fukin tashi

Kui aiki ku zam nishi

Ku cika aljihu ba bashi

Ku daina fama da rashi

Al’umma ta zam mai kwazon karsashi

 

A tabbatar da tsaro

A kawar da tsoro

Ai shuka ko dashen tsiro

A samar da hatsi tsagwaro

Wannan ke nunin kyakkawan horo

 

Liyafar uwar jiki

Tsafta ta zam babban aiki

Sharar farfajiya ta kai kuryar daki

Jibgin juji ya zam abin mamaki

Mutane mui ta aikin kirki

 

A assa masana’antu

A daina kulla kutu-kutu

Balle bera ya samu damar buruntu

A daina biyar rududu kar mutum yai huntu

Ai himma a samu hutu

 

Dazarar mun yi arba

Muna masu yi wa juna marhaba

Kowa ya samu kyakkyawar tarba

Kasa ta hau mafi kyawun turba

A hadu da juna ana haba-haba

 

An dai bayar da sautu

Masu karatu sui ta satu

Masu tabin kwanya a ce sun zautu

Mashirmata sui ta surutu

Laftun labarai rututu

 

Matattakalar takun gaba

A samar da tsibi-tsibin tsaba

A hana ’ya’ya ta’adar dabba

Magabta ai musu kawanyar zobba

Nagargarun ayyuka su zam mun saba

 

 

Haurobiyawa

Mu harhadu mu haye

Kar mu bari mu sha kaye

Hadakar karfin birni da kauye

Mu share hawayen ’yan uwa

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos