Tsoron Boko Haram ya sa ana hana ’yan Arewa gidajen haya a Legas

  Daga Masu gidajen haya a sassa da dama na Jihar Legas sun dauki matakin dakatar da ba ’yan Arewa hayar gidajensu saboda tsoron fadawa tarkon kungiyar Boko Haram.Mutanen da Aminiya ta tattauna da su a karshen makon jiya sun ce lamarin ya fi kamari idan mai neman hayar Bahaushe ne ko Babarbare.Malam Musa Muhammadu […]

Tsoron Boko Haram ya sa ana hana ’yan Arewa gidajen haya a Legas
Tsoron Boko Haram ya sa ana hana ’yan Arewa gidajen haya a Legas

 

Daga

Masu gidajen haya a sassa da dama na Jihar Legas sun dauki matakin dakatar da ba ’yan Arewa hayar gidajensu saboda tsoron fadawa tarkon kungiyar Boko Haram.
Mutanen da Aminiya ta tattauna da su a karshen makon jiya sun ce lamarin ya fi kamari idan mai neman hayar Bahaushe ne ko Babarbare.
Malam Musa Muhammadu ya ce “Idan ka je neman haya kiri-kiri za a ce ba za a ba ka ba saboda kai dan Arewa ne. Idan suka gane cewa kai Bahaushe ne ko Babarbare za su fito fili su gaya maka cewa dalilin da ya sa ba za su ba ka haya ba saboda suna tsoron ba dan kungiyar Boko Haram ne haya.”
Shi ma Malam Jibo cewa ya yi “Da suka je neman hayar gida a wani wuri sai aka ce musu ba za a ba su ba saboda su Hausawa ne, shi kuma maigidan ya ce ba zai ba Bahaushe gidansa ba saboda Boko Haram. Haka muka dawo ba mu samu daki ba balantana gida.”
Shi kuwa Malam Sale Isyaku cewa ya yi “Da kunnena na ji wasu masu gida suna cewa ba za su ba Bahaushe gidansu ba saboda akwai ’yan Boko Haram a cikinsu.”
daya daga cikin masu gidajen haya Tunde Adeyemi ya ce “Kada mutane su yi mana mummunar fahimta, hujjarmu ta kin ba wa ’yan Arewa haya ita ce muna tsoron kada mu ba wa ’yan Boko Haram ne. Ka dubi abin da ya faru a Unguwar Ijora inda aka samu ’yan Boko Haram a wani gida. Shi ya sa muke yin taka-tsantsan. Kafin na ba mutum haya sai ya kawo wanda zai
tsaya masa.”
Wata mai gidan haya mai suna Alaja Khadijat ta ce tsoron fadawa cikin matsala ya sa ba sa ba ’yan Arewa hayar gidajensu a Legas.