Tsoron shan-kaye ya hana APC gudanar da zaben kananan hukumomin Jihar Kaduna – Sulaiman Isa
Honorabul Sulaiman Isa (Baffa) tsohon Mataimakin Shugaban Riko ne a karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna a zamanin gwamnatin PDP, yanzu kuma mai taimakawa na musamman ne ga Sanatan Kudancin Kaduna, Sanata danjuma La’ah na PDP. A tattaunawarsa da Aminiya ya yi tsokaci kan halin da talakan Najeriya ke ciki, inda ya bayyana cewa […]
Honorabul Sulaiman Isa (Baffa) tsohon Mataimakin Shugaban Riko ne a karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna a zamanin gwamnatin PDP, yanzu kuma mai taimakawa na musamman ne ga Sanatan Kudancin Kaduna, Sanata danjuma La’ah na PDP. A tattaunawarsa da Aminiya ya yi tsokaci kan halin da talakan Najeriya ke ciki, inda ya bayyana cewa ba PDP ce ta lalata Najeriya ba. Kuma ya ce gwamnatin Jihar Kaduna ta ki gudanar da zaben kananan hukumomi ne don gudun irin kunyar da za ta sha idan aka gudanar da zaben a halin da ake ciki:
Me za ka ce game da salon tafiyar wannan gwamnati a matakin tarayya?
Ya kamata ne a ce idan an tsuke bakin aljihu kayayyaki su sauka, amma kuma sai ga shi kaya na ta hauhawa, ya kamata a nemi kwararru a kan harkar tattalin arziki su ba Shugaban kasa shawara da mafita domin gaskiya halin da ake ciki talaka ya fara cire rai da kuma yanke kauna da wannan gwamnati. Daga bari mu ga kwana dari sai a ce a ba da wata uku sai kuma a ce a kara hakuri bari mu ga shekara daya. Duk da kasancewata dan Jam’iyyar PDP, ba ina cewa duk abin da wannan gwamnati ke yi ba daidai ba ne, a’a, amma dai a rika cizawa ana hurawa. Kamar bangaren tsaro ai ya yi kokari kuma an samu ci gaba sosai kuma ni ma ina yaba masa ta wannan bangaren, hakazalika, bangaren maida asusun gwamnati bai-daya (TSA), shi ma wannan ba karamar nasara ba ce domin ko bai magance cin hanci da rashawa gaba daya ba, to zai rage kashi 90 cikinn 100. Amma ana kama wannan a kama wancan duk ba shi ne ba, akwai wuraren da ya kamata a duba domin talaka ya dan ji dadi ya samu inda zai sa kansa.
A matsayinku na ’yan adawa, me ya sa ba za ku ba gwamnatin APC uzuri mai tsawo kwatankwacin irin wanda aka ba ku ba, kafin ku fara korafi?
Ai PDP ba da haka ta fara ba, ina ganin ita wannan gwamnati kamar ba ta shirya ba ne tun farko, watakila ba su zaci za su karbi mulki ba ne. Idan ba haka ba, ai ba yau suka fara takara ba, tsawon shekara 16, tun kafin su zama jam’iyyar hadaka suke adawa. Tuntuni me suke yi da ba su shirya ba, ko da ma ba su da wani shiri ko tanadi ne a kasa na in sun karbi mulki me za su fara yi, daki-daki? Ba maganar rashin ba da uzuri ba ne, ai Bahaushe ya ce Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta. Mutum ko a gidansa ne in dai yana da tsari ya san daga ya yi wannan sai wancan abin ba zai rikice masa ba.
Wane hasashe kuke yi game da zaben shekarar 2019?
Ka san in kana da mata biyu daya tana yi maka tuwo daya kuwa ba ta yi, to ba za ka gane wacce ce tafi iya miya ba. Yanzu ’yan Najeriya su ne alkalan kansu, kowanne ya taba an ji irin nasa. Sun ji irin namu dandanon a PDP, sun ji irin nasu a APC, za su yanke hukunci a zaben gaba. Amma mu dai ga dukkan alamun da muke gani a kasa suna nuna mana cewa lallai mutane sun gane sun yi kusukure a zaben da suka yi domin har yanzu ba su gani a kasa ba. Kuma nakan ji ana ta cewa wai PDP ce ta lalata kasar nan, amma gaskiya ban yarda ba. Tarihi ai maimaita kansa yake yi, na san a lokacin mulkin soja, tun kan a halicci PDP, mutane har wanka da sabulun soda suka koma yi, sannan su shafa man inji. Don haka ban yarda da cewa PDP ce ta lalata kasa ba, kamata ya yi a ce da wannan gwamnatin ta hau, in har ba ta iya bunkasawa, to bai kamata ta kasa rike abin da ta tarar a yadda yake ba. In ka duba a lokacinmu iya tsadar shinkafa Naira dubu tara ne, amma yanzu ana sayen shinkafa Naira dubu 15, ka ga wannan rashin kwarewa ce ta fuskar tattalin arziki, don haka mu daina yaudarar kanmu, a nemo kwararru a fannin tattalin arziki su tallafa masa da shawarwari. Yawan almajiran da ake turawa bara yanzu, wallahi wasu ba don karatun ba ne domin iyaye su samu sauki ne.
Me za ka ce kan rashin gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar Kaduna?
Tsoro ne kawai, ba komai ba ne, sun firgita ne saboda alkawura da yawa da suka daukar wa mutane ba su cika ba, don haka suke tsoro suna so sai sun fara taba aiki, su saki wannan, su saki wancan sai a ce dama an lalata komai ne yanzu ne suka samu zarafi, to, wannan yaudara ce, a ce shekara daya har yanzu ana tantancewa ba a gama ba. A ce a je wajen Babban Akanta na jiha, an jima Gwamna ya ce ya biya ba mai binsa bashin ko sisi, ma’aikata sun zama abin tausayi kodayake ina dauka alhaki ne ke bin su, domin bayan duk irin gatan da muka yi musu, ba mu rike musu hakkokinsu ba, amma aka zo aka ce za a kara musu albashi, to yanzu akwai wadanda suka yi wata goma misali Dagatai da Hakimai, babu albashi. Yanzu ana so ne kawai sai lokaci ya yi a zo a sake rudar mutane da ’yan kwalbatoci da kankare titi a ce za a yi musu hanya a ce a zabe su. Yanzu kan mutane ya waye kuma alkalan kansu ne, ba wanda za ka ce sai lokacin zabe za ka masa kwalbati ko wani abu don ya zabe ka, an ga kamun ludayin kowa ba sai ka je kana wani kamfen ba.
Wadanne nasarori mai gidanka ya samu wajen kyautata rayuwar al’ummarsa?
Mun samu nasarori sosai, domin daga lokacin da Sanata danjuma La’ah ya shiga majalisa, ya raba kayayyaki a asibitoci. Akwai cibiyoyin kiwon lafiya da dama da ya kai musu kayayyakin asibiti da suka hada da gadaje da magunguna da firiji da janaretoci da sauransu, kamar a Jere da Kwagiri, kai duk kananan hukumomi takwas na Kudancin Kaduna, babu inda cibiyoyin kiwon lafiya biyu ko uku ba su samu irin wannan tagomashi ba. Kuma akwai wani shiri da ya yi na ba da horo kan koyon sana’o’i ga marayu da zawarawa da suka hada da koyon dinki da yin sabulu da sauransu kuma komai ya kankama a yanzu haka muna daukar sunaye ne da za mu fara. Akwai horarwa na musamman da kuma wasu kayayyaki na tsaro da za a ba ’yan banga kwanan nan don inganta tsaro kasancewar wurinmu ya yi kaurin suna wajen yawan samun tashin hankali ba za mu dogara kawai ga jami’an tsaro ba, wadannan kadan ne daga cikin irin nasarorin da muka samu.