Tsoron wuta

Wani Basakkwace ne da abokinsa ya gayyace shi, ya ce ya tara kudi za su je otel su kwana da mata. Rannan ya zo ya ce wa abokin ya shirya, su tafi. Da suka tafi suka kama daki a otel, aka sama masa abokiyar hira. Da ya shiga dakin sai ya kunna fanka, ashe fankar […]

Tsoron wuta
Tsoron wuta

Wani Basakkwace ne da abokinsa ya gayyace shi, ya ce ya tara kudi za su je otel su kwana da mata. Rannan ya zo ya ce wa abokin ya shirya, su tafi. Da suka tafi suka kama daki a otel, aka sama masa abokiyar hira. Da ya shiga dakin sai ya kunna fanka, ashe fankar ba ta da kyau sosai, sai ya ji tana kara tana cewa: “Sa’ir, sa’ir, sa’ir!” Sai ya kira abokinsa ya fada masa cewa: “Wannan fankar ta gane cewa zan yi lalata, shi ya sa take kira mani wutar sa’ir.” Abokin ya ce a canza masa daki, aka canza. A can da ya kunna, sai ta rika wurgawa da karfi, tana fadin: “Habu-habu, habu-habu!” Nan take ya fasa, domin Habu-habu ma suna wutar lahira ce. “Allah ne ya ganar da ni, don haka na fasa kwana a otel din nan, kada in je in kone.”
Daga Azzubair M. Fagge, 08034412272