Tsuguni-tashi ba ta kare ba
Bayan makwanni shida da sace ‘yan matan makarantar Chibok, duniya kuma na ta nuna damuwa game da haka, sai ga babban Hafsan mayakan kasar nan, Eya Mashal Aled Badeh ya ce an gano inda ake boye da su, amma ba zai tona asirin haka ba, kuma sojoji ba za su yi gaggawar kutsawa ba don […]
Bayan makwanni shida da sace ‘yan matan makarantar Chibok, duniya kuma na ta nuna damuwa game da haka, sai ga babban Hafsan mayakan kasar nan, Eya Mashal Aled Badeh ya ce an gano inda ake boye da su, amma ba zai tona asirin haka ba, kuma sojoji ba za su yi gaggawar kutsawa ba don ceto su saboda kada garin neman kiba a samo rama. Wannan labari ya sa iyayen ‘yanmatan da masu tausaya masu murna, sa’anan kuma jama’a da yawa sun yi mamaki game da haka ganin cewa ai tun da farko sojoji sun ce ‘yan matan sun komo gida, amma daga bisani kuma suka karyata, ba kunya, ba tsoron Allah.
Da farko dai tambayoyi suka yi ko da gaske ne an gano inda ‘yan matan ke boye? Shin yawan matsin lamba da aka yi ta yi masu ne a nan cikin gida da kuma kasashen ketare ya sa sojojin suka ce haka? A ganin jama’a ko ba tare da taimakon kwararrun jami’un tsaro daga kasashen ketare ba, sojojin Najeriya na iya gano inda ‘yan matan nan suke, ba tare da dogaro da jiragen sama da na’urorin leken asiri na kwararrun kasashen waje ba.
Wani abin mamaki game da haka kuma shi ne tun lokacin da aka fara hayagaga game da sace ‘yan matan nan gwamnati ba ta ce uffan ba dangane da irin kokarin da take yi na fitar da su daga cikin kangin da aka jefa su, duk kuwa da makudan kudaden da ake kashewa don ayyukan tsaro, kusan Naira miliyan dubu 130 cikin watanni hudu. Hakan bai karfafa gwiwowin jami’an tsaro don ci gaba da neman su ba, hasali ma Shugaba Goodluck Jonathan cewa ya yi kada a dame shi da wannan batun, masu kukan sace ‘yan matan na iya zuwa inda aka makanta su a ja masu gora.
Sai ga shi nan a daidai lokacin da ya yi wannan batun wata kungiyar da ke fafitikar goyon bayan rundunar mayakan Najeriya ta bulla, tana kwanzarta irin kokarin da suka yi don kwato ‘yan matan da kuma yin kira da babbar murya ga kungiyar Boko Haram da su hanzarta sako ‘yan matan. An ce gwamnatin Jonathan ce da kuma wasu kungiyoyin dagula al’amuran Najeriya na kasashen waje suka kafa wannan kungiyar don su nuna cewa gwamnati da jami’an tsaro ba su gaza ba a fafitikar kwato ‘yan matan Chibok. Ko a yanzu ma da aka ce wai an gano inda ‘yan matan suke, wata sabuwar hila ce ake ganin an bullo da ita da gangan don kada asirin ainihin wadanda suka yi awon gaba da su ya tonu. Al’amarin satar wadancan ‘yan matan ya zame siyasa domin kuwa makarraban Shugaba Jonathan na karyata batun, suna cewa kokari ne ake yi a shafa masa kashin kashi, a kuma taka wa gwamnatinsa birki.
An ce akwai wani dan jarida, amintacce wajen gwamnati da kuma kungiyar Boko Haram, Malam Ahmed Salkida da ya yi ta-maza, ya tunkari inda shugabannin kungiyar Boko Haram suke, ya isar da sakon gwamnati, ya kuma karbo wani daga ‘yan ta’addan cewa sun amince za su saki ‘yan matan da aka ce suna tsare da su muddin dai za a sako nasu fursunoninsu da ke hannun hukumomi. Da farko dai gwamnati ma ta amince da haka, ta kuma fara daukan matakan tattaunawa da wasu shugabannin ‘yan ta’addan, sai Shugaba Jonathan, ya yi kememe, ya ki amincewa da haka, ya kuma aiko da wani sakon dakatar da wannan yunkurin yayin da yake halartar wani taro a birnin Paris, inda aka hure masa kunne game da haka. Wata jaridar kasar Birtaniyya, ta ce wannan na daga cikin dalilan da ya sa ake rike da ‘yan matan har yanzu. To wai me shugaba Jonathan ke shakku ne game da sakin wadancan fursunonin, ko kuwa so yake ‘yan matan Chibok su tabbata cikin bakar wahala?
Uwargidar Gwamnatin Najeriya, watau Amurka, ta tabbatar da batun gano mabuyar wadanda suka sace ‘yan matan, ta kuma ce tilas ne a yi taka-tsantsan wajen kokarin kwato su, domin idan ba haka ba za a yi ba-wan-ba-kanin. Kaman yadda aka ji wani babban jami’in tsaron kasar na cewa, za a bukaci ingantattun kayayyakin aiki da na leken asiri, a kuma dauki dogon lokaci kafin a cimma burin kwato ‘yan matan salin-alin, ba tare da ko kwarzane ba, amma hanya mafi sauki ita ce ta yin musanyar ‘yan matan da fursunonin da suke so a saki. To amma sai dai Amurka ta ce ita ba ta goyon bayan darewa teburin sulhu tare da ‘yan ta’adda, kamar yadda Shugaba Jonathan ya jadadda. Ashe kuwa idan haka ne tsuguni-tashi ba za ta kare ba, za a ci gaba ne da gwagwarmaya a banza, iyayen yaran za su ci gaba da dawwama cikin bakin ciki, su kuma ‘yan matan za su tabbata cikin zullumin da zai iya halaka su. To wai me zai hana ne ba za a yi musanyar ‘yan matan da fursunonin da ‘yan ta’addan ke tsare da su ba? Ko kuwa babu su ne, duk an halaka su yayin da aka yi zargin sun nemi su tsere a Abuja? Haka dai shi ne mafi a’ala don kwantar da hankulan kowa da kowa.