Tsuke lalita ko tsukukun lalata?
A rana ta karamin lauje da tsayuwa bisa kafa daya,gawatan watan Noman-Baba na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwabisa kfa daya, na tashi da subahi sakaliya, ina sauraren,akwatin Magana na Babban Bakin Ce-ce Ku ce da ke birnin Lantsandanm, sai na ji wata karyayyar maganar Malam Mai yaren Hau-hau wajen hawan-sa ba […]
A rana ta karamin lauje da tsayuwa bisa kafa daya,gawatan watan Noman-Baba na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwabisa kfa daya, na tashi da subahi sakaliya, ina sauraren,akwatin Magana na Babban Bakin Ce-ce Ku ce da ke birnin Lantsandanm, sai na ji wata karyayyar maganar Malam Mai yaren Hau-hau wajen hawan-sa ba tare da sa-in-sa ba, inda aka ce: Kowa ya ji dadin gari,bai kai Babban mutum mai rawani ba.’ Ni kuwa sai na ce, wato za a iya cewa,”kowa ya shiga gararin gari bai kai talakamai fama datalalar talauci ba.” Don haka ’yan makarantar Dodorido za ku iya fasko cewa, shirin tsuke lalita da Gwamnatin Haurobiya tabullo da shi ba wani abu ba ne illa, tsukukun lalata.”
Haurobiyawa dai sun samu kan su acikin halin ha’ula’i, tun daga shekara ta alif silidamanuniyar kasa da taasdatakasa zuwa shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, inda jam’iyya maidan boto da sanda jirge ta shafe shekaru sili da tsayuwa bisa kafa guda tana mulkin mulaka’u, a karkashin tsarin damo-da-kura-dadiyya. Kowa ya san yadda akefama da yamutsin masu haramta Bobo da kwambon bokoko, har ta kai ga Haurobiyata zama’Babu tsaro sitsoro,’sannan ga tsarin tsimi da ta’adi da in-gwangwaje-in-wala da Mai-ganga-gangar kaso-kason-wawanci ke tsuwurwurtawa a kasar nan. Kuma saboda iya Majigin makafi na Gwamnatin Gudun-loko da Jona-tantin mulkin mulaka’u, sai aka yi ta yi wa al’ummar kasaDodorido,inda aka dora su akan shorido da cewa karfin dukiyar kasar Haurobiya ya fin a kowce kasa a fadin Ifrikiyya.Yau dai ga shi ta tabbata farashin man tunkuza ya yi warwas a kasuwannin duniya, don haka Gwmanatin Haurobiya ta bullo da shirin tsuke wa talakawa lalitarta, inda manyan ’yan lelenta suka lafe a cikin tsukukun lalata, suna ta lalata damin Hauro.
Haurobiyawa, a daidai lokacin da nike ta kokarin tattaradarussan farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai ta Dodorido, sai na samun labarin cewa, Gudun-wuni Gwamnan Babban Asusun Haurobiya ya kara kudin ruwa a kan lamunin da asusu-asusun kasar Haurobiyawa ke bai wa masu hada-hadar kasuwanci, sannan ya daga kimar darajar Dalar Hauron Amurkawa, inda ya dorata a kan Hauron Haurobiya sili da manuniyar sama da tukunyar dambu. Fargabar da ke damun al’umar Haurobiya itacetatsuga tsadar kayan masarufi, tayadda ’yan kwadago masu laluben kadago za su yi ta aiki tamkar agogo, amma sai su karke a kogon wahala.
Batu na ingarman karafa, in dai har ’yan adawa ba su shiga dawa ba, to kamata ya yi su kara himma wajen jefa mai dan boto cikin dawurwuri, musamman ma a daidai lokacin da rigingimun cikin gida suka baibayeta. Su kuma tabbatar mana da cewa, ba za a koma gidan jiya ba.
Haurobiyawa mun tambayi kawunanmu, shin yamutsin haramta bobo da kwambon bokoko shi ne garabasar dama-dama-dakurda-kurdar wasan Samson-siya-siya da kwakwalen al’umma da aka tarfa mana. Ko kuma majigin makafin da ake yi wa al’umma, tare da zuki-ta-malle kama-kare ka hada shi da zomo mai fala-falan kunnuwa. Don na tuna yadda tsohon Mai karanta Labaran Mako a fadar tsaunin Bila da ke Haurubja ya taba furta cewa, tun daga Haurubja har zuwa Jihar Bararon-nono babu kwazazzabai, domin mai gidansa ya shimfida kwalta ’yar taushi.
’Yan makaranta, wadanda ba su kakaba wa kurungunsu tagiyar Malam Mantau ba, za su iya tunawa a labaran duniyar damuka taba yi a farfajiyar wannan makaranta, aitaken da ka kada mana shi ne:
Tirikiti tirikit tititi
Mu mutanen Haurobiya
Kowa ya sha wuya
Hanyar mota da kwazazzabai
Ga jami’an tsaro na karbar ’yan kwabai
Masu na kasa ku farfado
Ja ya fado
Ja ya dauke
Masu mulki sun cafcafke!
To kun ga dai dabara ta rage wa mai shiga cikin kwakware, ko dai ku sake dawo damai dan boto da sanda jirge kan mulki, ita kuwa ta ci gaba da gasa muku ya a ka, ko kuma ku nemi masalaha. Don haka kowa ya yunkuro mu tabbatar wa miyagun masu shan gaban al’umma cewa,”Ba ma so! Mun gaji da tsukukun lalata dukiyar al’umma, inda aka fake da shirin tsuke lalita. Sannan mun gaji da tsarin kama-karya,taunacinye ka hadidiye. Tunda shugabahn kasar Haurobiya ya fi jin batutuwan su Asarar dan-kwabo da Kansakalin-kuku da Baudadden Joji da Dumu-Dumu Muzu-Muzu da Banga-Banga Tukururu, me zai hana a kyale shi da su, su kada masa kuri’a. Mu kuma gama-garin al’umma mu hana su sakat. Kuma wajibi ne a fito da tsarin kawar da duk wata jam’iyya ko daidaikun malalata da a kullum nufinsu su jefa al’umm a cikin garari.
daukacin mujallu da makalu dajaridun kasar Haurobiya suna yawan baza labaran ta’asar da ake tafkawa a wannan gwamnati, amma sai artabu suke yi da masu taku da kulki da Baraden Burgar gadi da sauran jami’an tsaro. To Malam Mai yaren Hau-hau wajen Hawan-sa batare sa-in-sa ba, ya ce “mugunta dai tamkar tsilla fitsari ne a fako.” Kai hatta jaridun daakewallafaakasarUban-Mama Jikan Kenyawa Jagoran Amurkawa, sun tabbatar da cewa, tunda aka kafa kasar Haurobiya,ba atabayin kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma ba,irin yadda makarraban wannan gwamnatin ke cin karensu babu babbaka. Don haka ni ban ga dalilin shirin tsuke lalita ba.
Kai ku zo mu yi tsallen badake, don nuna kiyayya ga miyagu masu kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma; mu yi gwagwa da gwagwarmaya da masu fashi da mukami ko da dabara, musamman ganin cewa Loma-a-murde ya zama muzurun Lami.Babbar manufarmu a kullum ita ce, tabbatar da juhala, don tabbatar da adala a daukacin fadin Haurobiya.