‘Tsuntsaye masu fuka-fukan zinari’
Manyan Gobe barkanku da Sallah. Tare da fata an sanya kayan sallah kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wasu ‘Tsuntsaye masu fuka-fukin zinari’. Labarin ya kunshi yadda rashin kunya ya jawo walakanci. A sha karatu lafiya. Taku: Gwaggo Amina Abdullahi Akwai wasu tsuntsaye kyawawa masu fuka-fukin zinari a wani rafi […]
Manyan Gobe barkanku da Sallah. Tare da fata an sanya kayan sallah kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wasu ‘Tsuntsaye masu fuka-fukin zinari’. Labarin ya kunshi yadda rashin kunya ya jawo walakanci. A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi
Akwai wasu tsuntsaye kyawawa masu fuka-fukin zinari a wani rafi wanda ruwa ke kwarara. A wannan rafin akwa wasu bishiyoyi da suke sauko da furanni masu kamshi. Kuma ruwa wannan rafi fari kal ne ga dandano mai dadi.
Wadannan tsuntsayen sukan je wurin domin shakatawa. Idan suka gama sai kowane daga cikinsu ya cire fuffike daya a kai wa Sarkin garin don nuna godiyansu.
Rannan sai wata marainiyar tsuntsu ta zo gurin, sai ta yi tunanin gina gidanta kusa da rafin. Ashe sun hangota. Sai suka hana ta gina gidan suka ce da ita ai su ne masu wannan rafin domin suna biyan kudin zamansu a wajen da fuka-fukin zinarinsu. Suka ce da ita tabar wajen.
Sai ta ce itama za ta biya da nata fuffiken. Sai suka kwashe da dariya. Suka ce ai ita ba ta da fuffuken zinari gwara ta bar wurin kafin ranta ya baci.
Sai ranta ya bace taje wajen Sarki ta kai karansu. Sarki ya aika aka kirasu ya musu gargadi kuma ya ce da su ai fuka-fukin da suke ba da wa bai yi ko kusa da sayan wajen ba, don haka su bar wajen domin marainiyar tsuntsun ta samu ta gina gidanta ko kuma a fille masu wuya. Hakan ko aka yi. Tsuntsuwar ta samu ta gina nata gidan.