Tsuntsu ya yi tafiyar kilomita dubu 10 a kwana 42
Wannan jinsin tsuntsu na tashi daga Arewacin Turai zuwa cikin Nahiyar Afirka.
Hamada wuri ne mai ban-sha’awa, inda tsuntsaye suke yawatawa a sassan duniya. Sai dai da yawan tsuntsaye na da al’adar yin kaura.
Kwanan nan, wani tsuntsu da ake kira Honey Buzzard ya bai wa mutanen yankin da yake mamaki bayan sun ga wuraren da ya yi tafiya cikin kwana 42 kacal.
Wannan jinsin tsuntsu na farauta suna tashi daga Arewacin Turai zuwa cikin Nahiyar Afirka a kowace shekara. Lokacin hijirarsu galibi yana farawa ne a watan Nuwamba.
Kuma zuwa watan Afrilu suna komawa daidai wurin kiwonsu da koyaushe suke amfani da shi. Dangane da hanyar kaurar tsuntsayen a shekara-shekara, mazauna Helsinki babban birnin kasar Finland suna da na’urar bin diddigin wannan tsuntsu Honey Buzzard.
Sun ce da hunturu ya zo, tsuntsun yakan tashi zuwa Kudu don neman abinci. Yawanci, wannan tsuntsu yana zama ne a yankin Nahiyar Afirka ta Tsakiya da ta kunshi wasu kasashe kamar: Kamaru da Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya da Chad da Kwango Brazzabille da Jamhuriyyar DimokuraDiyyar Kwango da Ekuatorial Guinea da Gabon da Sao Tome da Tsibirin Principe.
Duk da haka, wasu tsuntsaye masu sha’awar nisan zango suna zurfafawa zuwa cikin kasar Afirka ta Kudu.