Tsuntsuwa mai shekara 68 ta sake yin kwai
Wata tsuntsuwa da ake kira Laysan albatross da ta fi rayuwa a gabar Midway Atoll da ke Arewacin tekun Pasifik ta saka kwayaye 35 kuma ana ji ta kai akalla shekara 68 a duniya. Tsuntsunwar da aka kiyasta ta fi kowa ne irin halittar tsuntsu dade wa a duniya, bayan ta kyankyashe kwayayenta 30. Wannan […]
Wata tsuntsuwa da ake kira Laysan albatross da ta fi rayuwa a gabar Midway Atoll da ke Arewacin tekun Pasifik ta saka kwayaye 35 kuma ana ji ta kai akalla shekara 68 a duniya.
Tsuntsunwar da aka kiyasta ta fi kowa ne irin halittar tsuntsu dade wa a duniya, bayan ta kyankyashe kwayayenta 30.
Wannan tsuntsuwar albatross ta sake yin wani kwai a shekarta da ke Midway Atoll a sansanin dabbobin da suke barin inda suke zaune inda take wani karamin tsibiri mai nisan mil 1,200 Arewa maso Yamma a Jihar Hawaii ta Amurka a tekun Pasifik.
Masana halittu sun ce, akalla wannan tsutsuwar ta kai shekara 68 amma yin kwan nata ya sa kamar ba ta kai wannan shekarun ba.
An gano shekarun tsuntsuwa Albatross ta hanyar shekarun tsuntsuwar Akeakamai wanda suke rayuwa tare tun shekarar 2006.
A cawar hukumar kula da kifi da dabbobin dawa ta Amurka a yankin Pasifik, sun tabbatar tsuntsuwar ta sake yin kwai bayan binciken masana halittu.
Wannan tsuntsuwa da wanda suke tare Akeakamai suna dawowa sheka daya ne duk shekara a Midway Atoll. Yayin da masanan ke yi musu lakabi da aminan juna.
Tsuntsuwar Albatross idan ta saka kwai daya tana kyankyashe shi ne sama da wata biyu kafin ta sake samun wata biyar na rainon wadanda aka kyankyashe.
A wannan lokaci Albatross da Akeakamai za ta dauke ta lokaci tana kwanci a kan kwan, yayin da wasu tsutsayen ke fita kiwo a teku. Bincike ya gano cewa, albatross kafin ta yi sabon kwai ta kyankyashe kimanin 30 zuwa 36.
Binciken dai ya gano cewa, idan ’ya’yan tsuntsayen suka fara fara tsufa suna komawa wajen iyayensu.
Wani masanin halittu Kelly Goodale, ya ce akwai jinsin irin wadannan tsuntsaye na albatross a gabar tekun da suke rayuwa. Da zarar sun dawo kiwo duk za su hada kansu waje guda.
Akwai kusan tsuntsaye miliyan uku da ke rayuwa a gabar teku Atol, yayin da sama da miliyan 1.2 na jinsin albatross ne kamar yadda jami’an kula da dabbobin dawa suka sanar.
An dai gano wadannan jinsin tsuntsaye na rayuwa a yankin ne tun a 1956 lokacin da sojojin ruwan Amurka suka bude wani reshen sansaninsu a tsibirin Midway.
Kelly ya gano cewa, tsuntsuwar albatross tana da shekara 46 a shekarar 2002 bayan ya ziyarci yankin, a wancan lokacin tsuntsuwar tana matashiya.
Masanin halittun a shekarar 2006 ya ci gaba da binciken shekarun tsuntsuwar koyaushe tun lokacin.