Tsuntsuwa mai tashi
Wani yaro ne ya tambayi uwarsa, ya ce mata: “Mama ni wai don Allah ’yar aikin gidan nan tsuntsuwace mai tashi sama?” Sai ta ce masa: “Haba Sadik, mutum ce ba tsuntsuwa ba ce, ya za a yi ta tashi sama, amma me ka gani?” Sai ya ce mata: “Jiya ne da kika tafi unguwa, […]
Wani yaro ne ya tambayi uwarsa, ya ce mata: “Mama ni wai don Allah ’yar aikin gidan nan tsuntsuwace mai tashi sama?” Sai ta ce masa: “Haba Sadik, mutum ce ba tsuntsuwa ba ce, ya za a yi ta tashi sama, amma me ka gani?” Sai ya ce mata: “Jiya ne da kika tafi unguwa, sai na ji babana yana ce mata ‘ya ke tsuntsuwar zuciyata!’ Jin haka sai mamar tasa ta ce masa: “Gaskiya ne, tana tashi sama, domin wallahi yau za ta tashi ta tafi kauyensu don ubanta.”
DagaAbubakar Ibrahim Hassan Hadeja