Tsuntsuwar da ta yi tafiyar kilomita 13,560 cikin kwana 11

Sai dai kundin tarihin har zuwa yanzu bai amince da wannan bayani ba.

Tsuntsuwar da ta yi tafiyar kilomita 13,560 cikin kwana 11

Tsuntsuwa

Wata karamar tsuntsuwa tana can tana bayar da mamaki bayan da ta kafa tarihin tafiyar kilomita dubu 13 da 560 daga ranakun 13 zuwa 24 ga Oktoban da ya gabata.

Tsuntsuwar dangin tsuntsayen Bar-tailed godwit ta yi tafiyar ce daga birnin Alaska na kasar Amurka zuwa Jihar Tasmaniya ta kasar Ostireliya, kamar yadda kafar labarai ta AP ta ruwaito.

Tsuntsuwar wadda aka lakaba mata ‘jaririya’ a Alaska a lokacin bazarar Arewacin Hemisphere an yi amfani da wasu na’urorin da za su ba masu bincike damar bibiyar lokacin da za ta fara tafiya ta tekun Pacific kamar yadda mai kula da kungiyar BirdLife Tasmania, Mista Eric Woehler ya bayyana.

Kuma saboda tsuntsuwar karama ce ba a iya gane jinsinta ba tukuna.

Tsuntsuwar mai wata biyar da kyankyashewa, ta bar Jihar Alaska ce daga yankin Yukon Kuskokwin a ranar 13 ga Oktoba inda ta isa yankin Ansos Bay da ke Tsibirin Tasmaniya a Arewa maso Gabashin Ostireliya a ranar 24 ga Oktoba.

Wannan dai na kunshe ne a cikin bayanan da wata cibiyar kula da kaurar tsuntsaye ta Jamus (Germany’s Mad Planck Institute for Ornithology) ta fitar.

Sai dai har zuwa hada wannan rahoto ba a buga rahoton binciken ko nazari kansa ba.

Tsuntsuwar ta fara kadawa ta Kudu maso Yamma wajen kasar Japan kafin ta juya Kudu maso Gabas ta kan tsibirin Aleutiya na Alaska, kamar yadda wata taswira ta Cibiyar Pūkorokoro Miranda Shorebird da aka buga a kasar New Zealand ta nuna.

Kuma an sake gano tsuntsuwar a Kudu maso Yamma inda ta haye ta samaniyar da ke kusa da Kiribati da New Caledonia, sannan ta wuce ta cikin Ostireliya kafin ta juya kai-tsaye zuwa yammacin Tasmaniya, jiha mafi yawan jama’a a Kudancin Ostireliya.

Na’urar satilayet da ke bibiyar tsuntsuwar ta nuna cewa ta yi tafiyar kilomita dubu 13, 560 ba tare da ta sauka a kowane wuri ba.

“Ko dai wannan wani hadari ne ko tsuntsuwar ta bace ko kuma wani bangare ne na yin hijirar tsuntsaye, har yanzu ba mu gano me ke faruwa ba,” in ji Woehler, wanda yake cikin masu gudanar da binciken.

Kundin Tarihi na Duniya ya nuna mafi tsawon hijirar da wata tsuntsuwa ta yi don neman abinci ko hutawa shi ne na kilomita dubu 12 da 200 kamar yadda na’urar satilayet ta bibiya daga Alaska zuwa New Zealand.

An dauki wannan tafiya ce a shekarar 2020 a wani bangare na binciken shekara 10 da ya kunshi Jami’ar Fudan ta China da Jami’ar Massey ta New Zealand da kuma Kungiyar Global Flyway Network.

Kuma wannan tsuntsuwa ce ta karya nasarar baya da ta samu da tafiyar kilomita dubu 13 a kaurarta na bara, in ji masu bincike.

Sai dai kundin tarihin har zuwa yanzu bai amince da wannan bayani ba.

2025: ’Yan Najeriya suke bibiyar abin da shugabanni ke yi – Atiku

Abba ya sanya hannu kan kasafin kuɗin N719bn na 2025

Mutum 5 da aka fi ambato a 2024 a Afirka

Gwamnatin Borno ta horar da mata 162 sana’o’in dogaro da kai