Tubabbun Boko Haram sun yi rantsuwar mika wuya ga Gwamnati
Akalla mutum 156 wadanda suke tubabbun ‘yan Boko Haram ne sun yi rantsuwar mika wuya ga Gwamnatin Najeriya a wani shirin da gwamnatin ta shirya mai taken ‘Operation Safe Corridor’. Tubabbun sun fito ne daga yankunan da suke fama da rikicin Boko Haram na jihohin Borno da Yobe da Adamawa, sun yi rantsuwar ne a […]
Akalla mutum 156 wadanda suke tubabbun ‘yan Boko Haram ne sun yi rantsuwar mika wuya ga Gwamnatin Najeriya a wani shirin da gwamnatin ta shirya mai taken ‘Operation Safe Corridor’.
Tubabbun sun fito ne daga yankunan da suke fama da rikicin Boko Haram na jihohin Borno da Yobe da Adamawa, sun yi rantsuwar ne a gaban mai shari’a Nehizena Idemudia Afolabi na babbar kotun Tarayya da ke jihar Gombe.
Tubabbun dai sun samu horo a fanni daban-daban na koyon sana’o’i da aka yi masu na watanni 11 wanda hukumomin Gwamnatin Najeriya suka shirya.