Tubabbun ’yan Boko Haram 5,000 sun koma cikin jama’a

Babu ko mutum ɗaya da cikin tubabbun mayaƙan na Boko Haram da ya sake ɗaukar makami a cewar Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’ani Tsaro

Tubabbun ’yan Boko Haram 5,000 sun koma cikin jama’a

Wasu tubabbun mambonin Boko Haram

Mayaƙan Boko Haram aƙalla 5,000 da suka tuba sun koma cikin al’umma da iyalansu, a cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addabnci na Ƙasa.

Cibiyar, wadda ke ƙarƙashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’ani Tsaro ta bayyana cewa babu ko mutum ɗaya da cikin tubabbun mayaƙan na Boko Haram da ya sake ɗaukar makami.

Ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar cewa wata shida bayan kammala ba su horo da sauya tunanin tsofaffin mayaƙan, amma har yanzu babu labarin ko mutum ɗaya daga cikinsu da ya yi tubar muzuru.

Shugabar Sashen Daƙile Rikice-rikice Masu Alaƙa da Tsattsauran Ra’ayi (PVEA)  ta Cibiyar, Ambasada Mairo Musa Abbas, ce ta bayyana haka a yayin taron gwamnonin yankin Tafkin Chadi a Maiduguri, Jihar Borno.

Da take jawabi kan kula da masu ficewa daga Boko Haram da kuma  kawo ƙarshen kungiyoyi masu ɗaukar makamai, Ambasada Mairo ta jaddada muhimmancin amfanin da matakai da dabaru na bai-ɗaya a tsakanin gwamnonin ya kin domin magance matsalar tsaron.

Ta ce shirin Operation Safe Corridor da ke karɓa ta tare da sauya tunanin tubabbun ’yan Boko Haram ya yi nasarar sauya tunanin tsofaffin mayaƙan ƙungiyar guda 5,000.

A cewarta, Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) tana aiki da sarakunan gargajiya da malaman addini a duk ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin ƙasar nan domin sanya ido kan yanayin rayuwar tubabbun mayaƙan da suka dawo cikin al’umma.

Ta kuma jinjina wa tsarin da Gwamnatin Jihar Borno ta jagoranta kan tubabbun mayaƙan da masu tsattsauran ra’ayi.