Tubabbun ’Yan Boko Haram 560 Sun Fara Koyon Sana’o’i A Borno

Tubabbun mayakan Boko Haram 560 za su fara koyon sana’o’i da samun horo domin komawa cikin al’umma

Tubabbun ’Yan Boko Haram 560 Sun Fara Koyon Sana’o’i A Borno

A ci gaba da kokarin dawo da tubabbun mayakan Boko Haram cikin jama’a, rukuni na 8 da ya kunshi mutane 560 sun fara karbar horo a Maiduguri, Jihar Borno.

Babban makasudin shirin shi ne baiwa tsofaffin ’yan ta’addan sana’a da ilimin da suka dace domin samun sake shiga cikin al’umma.

Mashawarci na musamman kan harkokin tsaro a Jihar Borno, Birgediya-Janar Abdullah Ishaq (mai ritaya), ya ce za a koya wa tsofaffin ’yan Boko Haram din sana’o’i daban-daban kafin a mayar da su yankunansu don sake haduwa da ’yan uwan su.

A yayin horon, za su saurari laccoci daga kwararru daga jami’o’i da jami’an tsaro da hukumar wayar da kan jama’a da malaman addini da sauransu a tsawon mako biyu.

Bayan kammala shirin, za su karɓi abubuwan da aka tanadar musu  don taimaka musu wajen komawa cikin al’umma.

Janar Ishaq ya ce, “Wannan shi ne rukuni na 8, wanda kafin su an yi wa mutane 7,930.

“A wannan karon muna da mutane 560, sannan daga cikin mutane 7,930 da muka horar, ba mu sami wani rahoto mara kyau daga kowa ba.

“A koyaushe sakona shi ne, da zarar sun dawo cikin al’umma, su shiga cikin harkokin al’umma, walau na suna, da jana’iza, da Sallar Juma’a, a hada kai da juna.”

A cikin shekaru uku na shirin, an cimma nasarori da dama, ta fuskar komawar mutanen gona, da kuma dawowar zaman lafiya a bangarori da dama na yankunan jihar.