Tubabbun ’yan Boko Haram da ke taimaka wa sojoji sun tsere da makamansu

Tubabbun mayaƙan Boko Haram da aka horar da su suke taimaka wa sojoji yaƙar ƙungiyar a Jihar Borno sun tsere. Rahotanni sun bayyana cewa tubabbun mayaƙan su 13 sun tsere da makamai da baburan da aka ba su. Mayaƙan da suka tsere na daga cikin daruruwan ’yan Boko Haram da suka ajiye makamai suka mika […]

Tubabbun ’yan Boko Haram da ke taimaka wa sojoji sun tsere da makamansu

Tubabbun mayaƙan Boko Haram da aka horar da su suke taimaka wa sojoji yaƙar ƙungiyar a Jihar Borno sun tsere.

Rahotanni sun bayyana cewa tubabbun mayaƙan su 13 sun tsere da makamai da baburan da aka ba su.

Mayaƙan da suka tsere na daga cikin daruruwan ’yan Boko Haram da suka ajiye makamai suka mika kansu Ga hukumomin tsaro.

Jaridar Premium Times ta ruwaito wani mai bincike a Najeriyar Samuel Malik yana cewa tubabbun mayakan sun tsere ne  yankin Ƙaramar Hukumar Mafa a watan Satumba.

Jami’in ya bayyana wa kafar cewa bayan tserewarsa mayaƙan sun ɗauki bidiyo inda suke nuna makaman da suka tsere da su.

Tun bayan da sojoji suka fara murƙushe ’yan Boko Haram a shekarar 2015 mayaƙan ke ajiye makamansu su miƙa wuya ga jami’an tsaro .

Hakan ya bayar da damar horar da wasu daga cikin tubabbun tare da  sauya musu ɗabi’u.

Wasu daga cikinsu kuma aka sanya su cikin runduna ta musamman da ke taimaka wa sojoji murkushe barazanar tsaro.