Tubabbun ’yan Boko Haram za su soma aikin sharar titi a Maiduguri

Jarabta dai Allah Ya riga Ya jarabce mu da ita.

Tubabbun ’yan Boko Haram za su soma aikin sharar titi a Maiduguri

Wasu tubabbun ‘yan Boko Haram

Gwamnatin Jihar Borno ta bullo da wani shiri na bai wa tsoffin mayakan Boko Haram aikin share hanyoyin birnin Maiduguri, a wani mataki na sake mayar da su cikin al’umma domin ci gaba da rayuwa.

Gwamnatin ta ce wannan shiri wanda zai samar wa tsoffin mayakan abin dogaro da kai, zai kuma bayar da damar fahimtar juna tsakaninsu da al’ummomin da rikicin Boko Haram din ya shafa wanda ake fatan hakan saukaka al’amura idan aka mayar da su cikin al’umma.

RFI ya ruwaito gwamnatin na cewa, wannan shiri kuma wani mataki ne na neman gafarar al’ummar da rikicin Boko Haram ya shafa.

A cewar Dokta Kole Shettima na Cibiyar Raya Kasa da Bunkasa Dimokuradiyya, shirin zai samu nasarar mayar da tubabbun mayakan cikin al’umma musamman ganin yadda suke yi wa al’ummar hidimar tsabtace muhalli da kuma yadda suka kaskantar da kawunansu wajen gudanar da wannan aiki.

“A yanzu da ake sa su yi wa mutanen gari aikin sharar titi, ina ganin hakan zai kawo daidaito wajen neman gafarar al’umma cewa abubuwan da suka aikata a baya ba daidai ba ne, amma yanzu suna kokarin su dawo cikinsu a zauna tare.

“A lokacin da suka fito suna wannan aiki na sharar titi, mutane za su janyo su a jika, su yafe musu laifukan da suka aikata a baya.

Sai dai tuni al’ummar da rikicin Boko Haram ya shafa da shugabannin jama’a suka bayyana ra’ayoyi mabanbanta, inda wasu ke ganin cewa, ya kamata gwamnati ta yi taka-tsan-tsan a wannan shirin domin kuwa ba zai haifar da da mai ido ba a cewarsu.

A cewar wani Malam Adamu Dan Borno, “matsalar da muke fuskanta ita ce, a duk lokacin da gwamnati ta so aiwatar da wani abu, ba ta zama ta duba idan ta yi mai zai haifar, sai dai kawai ta dauki abun ta yi shi yadda take so.

“Saboda haka wannan ba zai ba da ma’ana mai kyau ba, don ta ya ma za a ce za su sallami wadannan mutanen [tubabban mayakan] su kawo cikinmu har suna yi mana shara a gari, wannan ba karamin kuskure ba ne, ya kamata a duba wannan al’amari.

Sai dai wasu na da ra’ayin cewa, tun da tsoffin mayakan na Boko Haram sun tuba, to ya kamata al’umma su rungume su a matsayin ‘yan uwansu mutananen kirki domin a cewarsu, rashin karbar su a cikin al’umma ka iya haddasa wata masifar.

Daga cikin masu cewa ya kamata a kai zuciya nesa, a yafe musu, akwai Bishop Naga Muhammadu, Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Jihar Borno, da ya ca ya zama dole a hakura a dawo da tubabbun mayakan cikin al’umma.

“Ya kamata a fahimce su, wadanda suka nuna halin tuba a karbe su, a zauna da su kuma a yi tafiya tare.

“Jarabta dai Allah Ya riga Ya jarabce mu da ita, mu fahimce su, su ma su fahimce mu, don muna iya mu zauna tare.

“Mu daina tunanin cewa idan su dawo cikinmu za su kara yin wata barnar ba, don duk mutumin da ya ce ya tuba, Allah Ya karba saboda haka mu ma sai mu karbi tubansu.

Masu fashin baki kamar Malam Hafiz Aminu Dayyiba, na ganin kamar ya kamata a yi taka-tsan-tsan kuma a bi shirin a hankali domin samun nasararsa.

“Ina ganin akwai bukatar a yi dogon nazari da shawartar masana kafin aiwatar da wannan shiri da ake so a yi.

“Don akwai yiwuwar su ’yan Boko Hara din da suka tuba idan ba a yi musu abin da suke so ba, za su ga cewa tuban ba shi da wani amfani. Sannan kuma wadanda suke kokarin tuba za su toge.

“Wannan fa shi ne abin da ake cewa gaba Kura baya sa yaki,” a cewar Malam Hafiz.

Sai dai RFI ya ruwaito cewa, duk wani kokari na jin ta bakin tsoffin mayakan ya ci tura, domin kuwa hukumomi sun hana a yi magana da su.