Tubar ’Yan Kalare Ta Rage Kwacen Wayoyi Da Haura Gidaje a Gombe

’Yan kalare sun je sun tuba a gaban kwamishinan ’yan sandan Jihar Gombe

Tubar ’Yan Kalare Ta Rage Kwacen Wayoyi Da Haura Gidaje a Gombe

Jami’an ‘Yan Sanda a harabar majalisar dokokin Kuros Riba

Kwamishinan Matasa da Wasanni na Gombe Adamu Inuwa Ibrahim ya ce mika wuyan da ’yan kalare suka yi a jihar ya rage matsalar sace-sace a gidaje da kuma kwacen wayoyi.

Adamu Inuwa ya shaida wa Aminiya cewa tsare-tsaren gwamnati kan matasa ya sa suka ga dacewar mika wuya domin zama mutanen kirki.

Ya ce tun da ya kama aiki ma’aikatarsa ta dahe wajen ganin an dauki matakan da suka dace don saita su, zama masu amfanar al’umma.

A cewarsa, ya kuna roki masu sana’oin hannu daban-daban da su dinga daukar yaran suna koya musu sana’oi domin su samu abun yi su daina tada hankali.

Ya ce a sakamakon haka, a makon jiya ’yan kalare suka je hedikwatar ’yan sanda suka tuba a gaban kwamishinan ’yan sanda tare da ajiye makamansu.

Daga nan sai ya ce nan gaba gwamnati za ta sake daukar matasa aiki na GOSTEC a karo na biyu domin su taimaka wa jami’an tsaro wajen hana ayyukan barna a jihar.