Tudor ya maye gurbin Sarri a matsayin kocin Lazio
Tudor ya taka leda a Juventus a matakin dan kwallo tsakanin 1998 zuwa 2007.
Lazio ta sanar da daukar Igor Tudor dan kasar Croatia a matsayin sabon kociyanta, bayan da Maurizio Sarri ya yi ritaya.
A Larabar makon jiya ce Sarri mai shekara 65, ya ajiye aikin, bayan da kungiyar ta yi rashin nasara biyar daga fafatawa shida a bayan nan.
Mataimakin koci, Giovanni Martusciello ne ya ja ragamar Lazio a nasarar da ta yi ta lallasa Frosinone 3-2 har gida ranar Asabar a gasar Serie A.
Tudor, mai shekara 45, ya horar da Marseille a bara, wadda ta kare a mataki na uku a teburin Ligue 1, wanda ya yi koci a Udinese da Hellas Verona a baya masu buga Serie A.
Tudor ya taka leda a Juventus a matakin dan kwallo tsakanin 1998 zuwa 2007, ke nan ya san babbar gasar tamaula ta Italiya ciki da wajenta.
Wasan farko da Tudor zai ja ragama shi ne ranar 30 ga watan Maris, lokacin da Lazio wadda take ta tara a teburi da tazarar maki hudu tsakaninta da gurbin ’yan Europa za ta karbi bakuncin Juventus.
Haka kuma a watan gobe Lazio za ta fafata gida da waje da Juventus a zagayen daf da karshe a Italian Cup.