…Tufafinmu na al’ada ya fi atamfa a ranar Bianou – Bututuwa

Uwargidan Attah Tambari, mai suna Ummu Amina, wadda aka fi sani da lakabinta na Bututuwa, ta ce, “A ranar Bianou mai atamfa ba ta zuwa inda muke, domin mun fi ta”.  Ta yi karin haske a kan aikace-aikacen mata a ranar bikin, inda ta bayar da fifiko a kan nau’ukan abincin da suke girkawa, tun […]

…Tufafinmu na al’ada ya fi atamfa a ranar Bianou – Bututuwa

BututuwaUwargidan Attah Tambari, mai suna Ummu Amina, wadda aka fi sani da lakabinta na Bututuwa, ta ce, “A ranar Bianou mai atamfa ba ta zuwa inda muke, domin mun fi ta”.  Ta yi karin haske a kan aikace-aikacen mata a ranar bikin, inda ta bayar da fifiko a kan nau’ukan abincin da suke girkawa, tun daga ranar takwas ga wata zuwa ranar maraita, wato tara ga watan cika-ciki ke nan.
Uwargidan ta ja hankalin maigidanta kan yin kurin maganar da ya yi kan Abzinawan Yamma, da ya ce ‘mun fi su yawa’, musamman dayake ita daga can ya auro ta.
Jin haka ya sa Attah Tambari ya ce, “Yanzu duniya ta sauya, domin in ka duba gidana har da Zabarmawa”.
Bututuwa ta bayyana wa Aminiya ayyukan da mata ke yi a ranar Maraita (ranar da jaruman Buzaye ke fita kwanan daji), wato tafiya Aleksis.  “Kafin maraita, sai mun yi alkubus da ginas da cukubus (dakakken garin dabino da cukwu da hatsi). A kuma yi gurasa, wadda da garin fulawa ake yi; sai algaragis da ket da naman tanderu. Idan maza suka sha ado na bakin kaya, mu kuwa sai murna, babu tsohuwa, ba yarinya, domin murna ce ta  Ashura (10 ga Muharram). Sai mu nufi Tudun kasa, wajen tarbo mazaje.
Ta karkare bayananta da yin kira kan lallai a rike kayan al’ada, domin a wannan ranar Atamfa da shadda ba komai ba ne. “Idan muka saki wannan al’ada, to kada su ce suna Agadas. A ranar Bianou mutum yana iya sanya kayan Jikka 200 (kimanin Naira dubu saba’in, N70,000), wadanda suka kunshi tari ribi biyu da turkudi da alabe da takalmi balka, wadannan su ne Agadas”. Inji ta.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan