Tufka da warwara game da mutuwar Ooni na Ife
Da safiyar Larabar da ta gabata ce aka wayi gari da labarin mutuwar daya daga cikin manyan sarakunan kasar Yarabawa, Ooni na Ife Oba Okunade Sijuwade. Wata majiya ta ce ya kwanta dama ne da yammacin Talatar da ta gabata. A ranar juma’ar da ta gabata ce matan Sarkin biyu (olori) da wasu ’ya’yansa suka […]
Da safiyar Larabar da ta gabata ce aka wayi gari da labarin mutuwar daya daga cikin manyan sarakunan kasar Yarabawa, Ooni na Ife Oba Okunade Sijuwade. Wata majiya ta ce ya kwanta dama ne da yammacin Talatar da ta gabata.
A ranar juma’ar da ta gabata ce matan Sarkin biyu (olori) da wasu ’ya’yansa suka fitar da shi daga fadarsa da ke garin Ile-Ife suka garzaya da shi zuwa wani asibiti a birnin Landan domin yi masa maganin ciwon da yake damunsa.
A shekaranjiya Laraba da rana kuma sai Majalisar masarautar Ife ta fito fili ta karyata labarin mutuwar sarkin, duk da cewa a sanyin safiyar wannan rana kafofin labarai suka yayata cewa rarkin ya mutu ne da yammacin ranar Talata a wani Asibiti da ke Landan. A daidai lokacin da daruruwan mutane maza da mata suka samu labarin mutuwar sarkin sai suka yi dafifi a fadar Oodua a garin Ile-Ife, domin tabbatar da mutuwar sarkin nasu.
Bayanin da mai magana da yawun masarautar Ife wato, Lowa na Ife Oba Joseph Ijaodola ya yi wa ’yan jarida a ranar ta Laraba, ya ce Oba Okunade Sijuwade yana nan da ransa lami lafiya bai mutu ba kamar yadda kafofin labarai suka bayyana. Ya ce fadar Oodua ce kadai ke da alhakin sanar da mutuwar Sarki.
Shi ma sakataren majalisar masu rike da sarautun gargajiya na masarautar Ife, Ladin na Ife, ya ce: “An baza irin wannan jita-jita a cikin shekarun 1984 da 2004, yanzu kuma sun dawo da wata sabuwar jita-jitar. Oba Okunade Sijuwade yana nan cikin koshin lafiya.”
A ranar 6 ga watan Disamba na shekarar 1980 aka mika wa Ooni na Ife sandar tabbatar da nadinsa bisa wannan sarauta. Ya hau karaga ne kafin a kirkiro Jihar Osun daga tsohuwar Jihar Oyo a cikin shekarar 1991. Babbar matsalar da ya fara fuskanta ita ce, jayayyar shugabancin majalisar sarakuna a tsakaninsa da Alaafin na Oyo da kowannensu yake ikirarin cewa shi ne ya cancanci rike kujerar shugaban majalisar sarakuna na dindindin a wancan lokaci. Bayan kirkiro Jihar Osun daga tsohuwar Jihar Oyo, marigayi Ooni na Ife da Alaafin na Oyo, sun ci gaba da fifita kansu a kan sarakuna Yarabawa baki daya, wanda haka ya haifar da rabuwar kawunan sarakuna zuwa bangaren Ooni da bangaren Alaafin.
Wannan al’amari ne ya janyo babbar matsala a tsakanin dattijan Yarabawa da masu fada aji da ’yan bokonsu da ’yan siyasa da har yanzu suka kasa dinke wannan baraka da ta raba su gida biyu a matsayin magoya bayan wadannan sarakuna biyu da suke jayayyar jagorancin al’ummarsu.
Ta bangaren Gwamnatin Tarayya kuwa, kamar yadda jaridar The Nation ta jiya ta ruwaito, Babban Jakadan Najeriya a Ingila, Alhaji dalhatu Sarki Tafida ya ziyarci gidan Ooni a Ingila, inda ya ce ya kwashe awa daya tare da babban dan sarkin, Adetokunbo. Ya ce ya je gidan ne domin gaisuwar ta’azziyar rasuwar sarkin na Ife.