Tufka da warwarar Balarabe Musa
Kalaman Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a kafafen yada labarai game da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na iya haifar da rudani a tsakanin talakawa, don haka a wannan jarida taku mai albarka zan yi tsokaci a kan irin tufka da warwarar da tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna ya yi a gidajen jaridu game da rabon mukamai […]
Kalaman Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a kafafen yada labarai game da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na iya haifar da rudani a tsakanin talakawa, don haka a wannan jarida taku mai albarka zan yi tsokaci a kan irin tufka da warwarar da tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna ya yi a gidajen jaridu game da rabon mukamai a gwamnati. A jaridar Aminiya ka fito karara kana nuna goyon bayanka ga gwamnatin, har kana gaya wa duniya cewa “Goyon bayan Buhari wajibi ne,” sai kuma ga shi a Jaridar Rariya ta 28 ga Agusta (28-3/9/2015), shafi na shida (6) kana sukar gwamnatin, inda kake ikirarin cewa Gwamnatin Buhari tana fifita ’yan Arewa; sabanin mutanen Kudu, wato Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, musamman a wajen rabon mukamai.
Abin takaici ma har kana nuni da cewa ’yan Kudu maso Gabas na kukan ana nuna musu wariya.
Kasancewar Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa dan Jam’iyyar PRP, ina so in yi maka tambihi a kan wata magana da tsohon jagoran PRP na kasa ya taba yi, wato marigayi Malam Aminu Kano (Allah Ya kara masa rahama), inda yake cewa: “Najeriya daya ce, amma kowa ya san gidan ubansa.” Shin wannan karatu da Malam ya biya mana yaya za a yi, ko tarihi ne kawai; ko dai manta shi aka yi? Tuni ka fi ni sanin cewa gwamnatin Buhari zababbiya ce: mutane ne suka zabe ta, ba gwamnatin soja ba ce. (da kan dare karagar mulki in an yi juyin-mulki), dole sai an kyautata wa kowane bangare, ta hanyar kwantar da hankalin al’umma. Ya kamata ka fahimci cewa siyasa ba yanzu ake yin ta ba
Kuma tsarin rabon mukamai ya dogara ne da irin gudunmawar da kowane yanki ya ba da. Abin da gwamnatin da ta gabata ta yi, ba wai kawai a bangaren rabon mukamai ba, har da karya tattalin arzikin Arewa ta yi. Ta debi sama da matasa dubu biyar a bangaren Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma ta tura kasashen waje domin koyo sana’a. Ta musanya muhimman ayyuka da aka bai wa Arewa, shin ka taba cewa komai a kai? A bayyane yake har yanzu jama’ar Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas siyasar kabilanci suke yi da ta addini da bangaranci. Hasali ma dai har yanzu ba su yarda da kasancewar Najeriya daya ba, sai don dole. Har yanzu ba su daina barazanar ballewa ba, har yanzu gidan rediyonsu na Biyafara bai daina caccakar wannan gwamnati ba.
Da ka ce an nuna musu wariya, ai su suka ware kansu. Misali a zaben shekarar 2011; lokacin PDP da CPC, kuri’a nawa Buhari ya samu a duk fadin jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas? kuri’a Dubu 70 da kwaya ashirin da shida (70,026). Kai akwai ma jihar da kuri’a dari shida da casa’in da daya (691) kawai ya samu. Akwai adalci a hada su da jihar da miliyan daya da dubu dari shida ta ba shi? A zaben 2015, ba ta sake zane ba, domin kuwa shi ma duk fadin jihohinsu, duk da guguwar sauyi da kasar ta fuskanta, da matsalolin da al’ummar kasar suka fuskanta, APC kuri’a dubu dari shida da goma sha shida da dari takwas da talatin da takwas kawai ta samu (616,838). Wacce gwamnatin ma ta APC ce, kuma dan uwansu Gwamna Rochas ne ke mulkinta, kuri’a dubu dari da talatin da uku da dari biyu da hamsin da uku kawai ya samu. Akwai ma jihar da ya samu kuri’a dubu biyar da dari daya da casa’in da hudu kawai.
A yayin da wasu jihohin a wasu shiyoyin na kawo miliyoyin kuri’u. Ina so ka sani, ba Buhari ya ware su ba, ’yan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, su suka ware kansu, wannan batu dan uwansu Rochas ya fada musu. Ni dai na san Buhari adali ne, mai gaskiya ne, mai amana ne da sanin ya kamata. Kuma mukamai a Gwamnatin Tarayya, kamar yadda aka sani ne yanzu aka fara. Har yanzu lokaci bai yi ba da za a rika gutsiri-tsoma da kananan maganganu irin wadannan.
Kada a kawo mana rudani a tsarin wannan tafiyar. Talakawa sun gamsu da wannan gwamnati, kai hatta ’yan adawa ma sun mika wuya.
Zan rufe da fadin Manzon Allah (SAW), inda ya ke cewa: “Ka fadi alheri ko ka yi shiru.” A matsayinka na tsohon Gwamna, kai uba ne, kuma jagoran al’umma. Maganganun da za ka fadi su talakawa ke sauraro, irin wadannan kalamai ka iya ba da wata kofa, ko harzuka jama’a da janyo rudu a tsakanin al’umma, musamman kamar yadda ka sani yanzu zamani ya sauya, mai da martani ka iya jawo matsala. Ya dace a rika taka tsan-tsan da irin wadannan kalamai domin a karni na canji ake, kuma dole ne kowa ya girbi abin da ya shuka.
Ibrahim Ahmad Harisu Giginyu ya rubuto makalarsa ne daga Kano 07035636256.